Tsohon shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya bukaci Majalisar Dattijai da kada ta amince da Lauretta Onochie a matsayin kwamishiniyar zabe.
Lauretta dai na cikin wadanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da sunansu kuma Majalisar Dattijai ta tantanace su ranar Alhamis.
- Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya kara aure
- Yadda Masari ya ba daliba mai fasahar zane-zane tallafin karo karatu
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa sakamakon tantancewar zai fito ranar Talata.
Farfesa Jega, wanda ya bayyana a cikin shirin siyasa na Sunday Politics a gidan talabijin na Channels ranar Lahadi ya ce, “Wannan kace-nacen abu ne da za a iya kauce masa. Duk wanda nadinsa ya janyo irin wannan cece-kucen, kamata ya yi a yi taka-tsan-tsan saboda kasancewarsa a hukuma irinta INEC zai iya kawo nakasu ga sahihancin aikin hukumar.”
Ya ce Shugaba Buhari na da damar da zai iya janye sunanta ya maye gurbinta da wata macen daban daga jiharta.
Tsohon shugaban na INEC ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin ta Kasa kan yunkurin da ta yi na yi wa Dokar Zabe ta Shekara ta 2010 kwaskwarima, amma ya nuna rashin jin dadinsa kan cire aike wa da sakamakon zabe ta intanet zuwa rumbun adana bayanai na INEC.
Ya ce matakin da majalisar ta dauka zai yi mummunan nakasu ga ci gaban da aka samu a harkar zabe a Najeriya.
Nadin Lauretta dai, wacce tsohuwar hadimar Shugaba Buhari ce, ya tayar da kura matuka inda kungiyoyin fararen hula da ’yan adawa ke zarginta da kasancewa ’yar jam’iyyar APC.
Mutane da dama dai sun ce bai kamata ta zama kwamishiniyar zabe ta INEC ba saboda alakarta da APC.
To sai dai duk da sukar da ake ta yi a kai, Buhari yaki ya janye sunanta daga jerin wadanda yake son nadawar.