Tsohon mai jan ragamar mutanen da suka fi kowa kuɗi a duniya, Jeff Bezos ya maye gurbin da ya bari shekaru uku da suka gabata.
Jeff Bezos wanda shi ne wanda ya assasa kamfanin hada-hadar kayayyaki na Amazon, ya karɓe ragamar ne daga hannun Elon Musk.
- Daurawa ya shiga ofis bayan dawowarsa Hisbah
- An Dauki Nauyin Karatun Matashin Da Ya Mayar Da Tsintuwar N15m A Kano
Lamarin dai kamar yadda alƙaluma suka nuna na zuwa ne bayan hannayen jarin Elon Musk na kamfanin Tesla ya faɗi da kashi 7 da ɗigo biyu cikin ɗari a ranar Litinin.
Ma’aunin hamshaƙan masu kuɗi na Bloomberg ya nuna cewa, a yanzu Musk yana da arzikin da yawansa ya kai dalar Amurka 197.7 biliyan, yayin da shi kuma Bezos ke da dala 200.3 biliyan.
Haka kuma, wannan ne karon farko da Jeff Bezos mai shekara 60 a duniya, ya ɗare wannan matsayi na hamshaƙan masu kuɗin duniya na Bloomberg tun shekarar 2021.
Giɓin duniya da ke tsakanin Musk, mai shekara 52 a duniya da kuma Bezos, wanda a baya ya kai dala $142 biliyan, yana raguwa yayin da hannayen jarin Tesla da Amazon ke yin hannun babbar riga.
Duk da cewa duka kamfanonin biyu na daga cikin waɗanda suka fi bunƙasa kasuwar shunku ta Amurka, sai dai hannayen jarin Amazon ya ruɓanya tun shekarar 2022 ya zamo mafi ƙarfi.
Yayin da na Tesla kuwa ke faɗuwa da kusan kashi 50 cikin ɗari tun bayan ganiyarsa a shekarar 2021.
Dan Faransa shugaban kamfanin kayan ƙawa da alfarma na LVMH, Bernard Arnault, shi ne har yanzu a matsayi na uku a jerin masu arziki na duniya, inda darajar kuɗinsa ta kai dala biliyan 197.