✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jarumin Kannywood Ubale Wanke-Wanke ya rasu

Allah Ya yi wa tsohon fitaccen jarumin Kannywood, Ubale Ibrahim wanda aka fi sani da Ubale Wanke-Wanke, rasuwa. Manyan jaruman masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood…

Allah Ya yi wa tsohon fitaccen jarumin Kannywood, Ubale Ibrahim wanda aka fi sani da Ubale Wanke-Wanke, rasuwa.

Manyan jaruman masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood kamar su Ali Nuhu da Sani Danja da Yakubu Muhammad da Ishaq Sidi Ishaq da sauransu ne suka jagoranci sauran ‘yan masana’antar wajen yin ta’aziyya da nuna alhinin rashin mamacin.

Da yake bayyana alakarsa da mamacin, Yakubu Muhammad ya ce, “Muna bude-baki ya kira ni muka yi magana a kan da safe za mu hadu.

“Da ya yi sallar Isha’i suka ci abinci tare da abokansa a unguwarsu, sai ya yanke jiki ya fadi. Matarsa ta kira mu, muka tafi asibiti, muna isa asibiti likitoci suka bayyana mana ya rasu.”

Yakubu ya kara da cewa duk da Ubale ya girme su a shekaru, kasancewar a kamfaninsu na 2 Effects yake a Kannywood, ya kasance mutum wanda ba ya gajiyawa wajen hidimarsu,

“Mutum ne wanda ba shi da girman kai da dagawa.”

Tuni aka yi jana’izarsa a Kano kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Marigayi Ubale, ya kasance yana aiki da kamfanin 2 Effects, mallakar Sani Musa Danja da Yakubu Muhammad.

 

Wasu daga cikin ‘yan Kannywood da suka je ta’aziyyar Ubale
%d bloggers like this: