A yanzun nan ne Aminiya take samun labarin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu ko Ƙarƙuzu na Bodara.
Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako da jarumi a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Shi ma dai fitaccen jarumin Kannywood kuma Shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu, ya wallafa hoton marigayi Ƙarƙuzu a shafinsa na Facebook yana mai roƙon Allah Ya jikansa.
Ƙarƙuzu dai tsohon jarumi ne a masana’antar Kannywood da ya yi tashe tun a shekarun 1980.
Ana iya tuna cewa wata hira da ya yi da Zinariya TV kuma Mujallar Fim ta wallafa a shekarar 2023, Ƙarƙuzu wanda ya nemi taimakon jama’a ya sanar da cewa ya makance kuma yana fama da matsananciyar rashin lafiya.
Jarumin ya rasu cikin daren Talatar nan a birnin Jos bayan fama da rashin lafiya na tsawon shekaru wanda har ta sa ya makance.
Za a gudanar da jana’izarsa da safiyar gobe Laraba a garin Jos.