✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumin fim din ‘The Transporter’ ya bayyana goyon bayansa ga Falasdinawa

Jason Statham ya lullube lullube marfin injin motarsa da tutar kasar Falasindinu, da kuma ado da rawani don nuna goyon bayansa ga Falasdinawa

Fitaccen jarumin fina-finan Amurka na Hollywood, Jason Statham, wanda ya ja ragamar fim din ‘the Transporter’ ya nuna goyon bayansa ga Falasdinawa a yayin da Isra’ila ke musu luguden bama-bamai  a Zirin Gaza.

Jason Statham na shan yabo bayan bullar wani bidiyon a Twitter inda aka ga ya lullube daukacin marfin injin motarsa ta alfarma kirar GMC, da tutar kasar Falasindisu.

The Transporter bai tsaya nan ba, a cikin bidiyon dai an gan shi da kansa yana nada wa maduban gefen dankareriyar motar tasa mayafi da kyallen rawanin Falasdinawa.

A wani abu mai kama da fito-na-fito da mahaifarsa Birtaniya da kuma Amurka da yake rayuwa, bidiyon motar jarumin da ya taka rawa a fim din Furious 7 ya kuma fita unguwa da motar daga wani wuri mai dauke da tutar Amurka.

Wannan abu dai ya jawo masa yabo daga sassan duniya, saboda jarumtar da ake ganin ya yi a lokacin da Amurka da Birtaniya suke nuna goyon bayansu ga Isra’ila, wadda ta shafe makoni uku tana wa Falasdinawa ruwan bama-bamai a Zirin Gaza.

Sai dai duk da yabon da jarumun ke sha, ya zuwa wannan lokaci dai manyan kafofin yada labarai ba su rawaito lamarin ba.