✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jarumin Bollywood Kader Khan ya rasu yana da shekara 81 a duniya

Fitattacen jarumin fina-finan Bollywood, Kader Khan, ya rasu yana da shekara 81 a duniya. Rahotanni daga India sun ce ya rasu ne a asibitin Canada…

Fitattacen jarumin fina-finan Bollywood, Kader Khan, ya rasu yana da shekara 81 a duniya.

Rahotanni daga India sun ce ya rasu ne a asibitin Canada bayan ya dade yana fama da wata rashin lafiya da ta shafi kwakwalwa.

Kader Khan wanda musulmi ne ya fito a fina-finai sama da 300 na Bollywood a tsawon rayuwarsa BBC ta ruwaito.

Tun a 1973 ya fara fim inda ya fito a wani fim mai taken ‘Daag’ tare da shi da Rajesh Khanna da Sharmila Tagore.

Yana fitowa a matsayin bos da kuma uba kafin ya koma yana wasan barkwanci a wajajen 1990.

Kader Khan ya dade yana rubuta labarin fina-finai kafin ya fara fitowa a fim.

Ya rubuta labarin fina-finai da dama da suka yi fice, kamar ‘Coolie’ da ‘Amar Akbar’ da ‘Mukaddar Ka Sikandar.’

A birnin Kabul na Afghanistan aka haifi Kader Khan, daga baya iyayensa suka koma Mumbai yana karami.

Abokan aikinsa a harakar fina-finansa da dama ne suka bayyana alhinin rashin Kader Khan.

Fitaccen jarumin fina-finan Bollywood Amitabh Bachchan ya bayyana rasuwar Kader Khan a matsayin babban rashi inda ya ce ya samu nasarori a basirar fina-finansa da ya rubuta.