Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, Blessing Ebigieson, ta gwangwaje zawarawa da tsofaffin mata da kyautar Naira miliyan bakwai a Zariya, albarkacin zagowar ranar masoya ta duniya.
Bikin dai an fara shi ne a masarautar Zazzau kafin daga bisani aka zarce Sabon Gari don ci gaba da shi, sakamakon masarautar na ci gaba da alhinin rasuwar marigayi Magajin Garin Sakkwato.
Jarumar ta ce tallafin na daga cikin shirye-shirye da gidauniyarta ta shirya don tallafa wa tsofaffi da zawarawa a fadin kasar nan.
“Shirin na daga cikin tsare-tsaren gidauniyar nan, amma wannan shi ne karo na farko da muka fadada shi zuwa Arewa.
“Babban burin shirin shi ne tallafa wa zawarawa, tsofaffin mata, don nuna musu kauna da jinkai, kuma a tafi da su a dukkan harkokin yau da kullum.
“Gidauniyar na yin wannan shiri a fadin kasar ba tare da nuna banbancin kabila, yanki ko addini ba. Mun yarda cewar dukkanin wani talaka na bukatar rayuwar mai inganci,” a cewarta.
Jarumar ta ce gidauniyar za ta fadada ayyukanta zuwa sauran sassan arewancin Najeriya.
A na shi wajabin, Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, wanda ya samu wakilcin Dan Barhin Zazzau, Alhaji Ahmed Bashir Aminu, ya jinjina wa gidauniyar kan yadda ta zabi masarautarsa wajen tallafa wa masu karamin karfi.
Kazalika, ya ba wa gidauniyar tabbacin goyon bayansa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.