✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumar Kannywood, Diamond Zahra ta amarce

Jarumar, wadda a yanzu take lokaci ta yi aure ne a karshen makon jiya.

Jarumar masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Zahra Muhammad, wadda aka fi sani da Diamond Zahra ta amarce.

Jarumar, wadda a yanzu take lokaci ta yi aure ne a karshen makon jiya kamar yadda Aminiya ta samu labari.

Jaruma Bilkisu Abdullahi ce ta bayyana hakan a shafinta na Instagram, inda ta sanya hoton Diamond Zahra din sannan ta ce, “Allah Ya ba da zaman lafiya kawata, Allah Ya albarkaci aurenku.”

Jaruma Diamond Zahra ita ce ke jan fim din ‘Gargada’ wanda Ali Nuhu ya dauki nauyi, sannan tana cikin fim din ‘Farin Wata’ na Adam A. Zango.

Yanzu haka ana cigaba da daukar shirin na Farin Wata, inda wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an musanya jarumar da wata.