✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jaruman Kannywood da aka daina jin duriyarsu

Sauran jaruman da suka yi nukusani sun hada da Mohammed Farar Aniya da Halima Abubakar.

A makon jiya, Aminiya ta kawo rahoto kan wasu furodusoshin Masana’antar Kannywood da suka shahara a baya, amma yanzu aka daina jin duriyarsu duk da cewa suna nan da ransu.

A wannan makon, Aminiya ta zakulo wasu jarumai maza da mata da suma aka daina jin duriyarsu a masana’antar.

Aminu Ilu Danbaza

Aminu Ilu wanda aka fi sani da Aminu Acid jarumi ne da ya yi fice a zamaninsa, wanda daga baya ya koma makaranta a Ibadan, inda ya karanci bangaren kiwon lafiya.

Yanzu haka yana aiki ne da Gwamnatin Jihar Kano.

Daga cikin finafinan da ya yi akwai Hakilo da ya yi tare da Hadiza Kabara da da Al’ajabi da Ajizi da Nadama da sauransu.

Abubakar Shehu

Abubakar Shehu jarumi ne da ya yi fice musamman a finafinan Jos a Kamfanin 3SP.

Sai dai yanzu ya zama Darakta a Kamfanin 3SP din.

Daga cikin finafinan da ya yi a baya sun hada da Wane ne da Azal da Kaddarah da sauransu.

Shi ne daraktan wakokin Sambisa. Haruna Talle Maifata Haruna Talle Maifata, jarumi kuma furodusa a kamfaninsa na Maifata Movies da ke garin Jos.

Ya fito a finafinai da dama irin su Zuciyata da Hafsa ko Safiya da Farmaki da Giwar Karfe da Dan Talaka da Gidan Maza da Gidan Alkali da Farida Nabil.

Bello Mohammed

Bello Fitaccen jarumi ne kuma darakta a garin Jos, wanda yana cikin jagororin fim a Jos da ya yi sanadiyar shigowar jarumai da dama Masana’antar Kannywood.

Daga cikin finafinan da ya yi akwai Uwar Miji da Rai da Saki Uku da sauransu shi ma ya yi nukusani.

Tanimu Akawu

Tanimu Akawu shi ma fitaccen jarumi ne da ke fitowa a matsayin uba a Masana’antar Kannywood.

Ya fi fitowa a matsayin mugu. Ya fito a finafinai irin su Ga Duhu Ga Haske da Artabu da Jarumin Maza da sauransu.

Zainab Indomie

Zainab Indomie ta yi zamani da jarumai da dama irin su Ali Nuhu da Adam A. Zango.

Sai dai an daina jin duriyarta na tsawon lokaci. Sai dai yanzu ta dawo inda aka fara ganinta a fim din Alaka mai dogon zango na Ali Nuhu, wanda ya faranta wa wasu masu bibiyar fim din rai.

Sani Musa Mai Iska

Sani Musa Mai Iska, tsohon jarumin Masana’antar Kannywood ne da ya auri jaruma Fati Mohammad har suka tafi Ingila tare. Ya yi fice wajen rawa na zamani a finafinan da.

A fim din Ashiru Nagoma mai suna Tururuwa ne ya fito bayan dawowarsa daga Ingila, sai dai kuma daga baya an daina jin duriyarsa baki daya.

Bashir Bala Ciroki

Bashir Bala Ciroki jarumin barkwanci ne da ya dade yana jan zare a masana’antar kafin aka daina jin duriyarsa.

Ana cikin tunanin ina yake ne kwatsam aka samu labarin ya koma sayar da kunu a Kano domin samun na sakawa a bakin salati.

Yanzu haka yana dan fitowa a wakokin Dauda Kahutu Rarara.

Sauran jaruman da suka yi nukusani sun hada da Mohammed Farar Aniya da Halima Abubakar da Ahmed Sadeek da A’isha Abubakar da Sadiya Mohammed wacce aka fi sani da Sadiya Gyale.

Akwai kuma Halisa Mohammed da Mohammed B. Umar, wanda aka fi sani da Hankaka da Karkuzu da Hussain Sule Koki da Abdulkadir Maje da ya yi fim din Sai A Lahira na Balaraba Ramat da Suleiman Alaka da Aliyu Sambo da Jazuli Mukaddas.

Kazalika, akwai irinsu Ibrahim Mohammed Gumel da Halisa Mohammed da Abdullahi Zakari (Ligidi) da Jinjiri da Shu’aibu Idris Lilisco da Fati Baffa (Fati Bararoji) da Hafsat Shehu da Nura Imam da Hajara Abubakar (Dumbaru).