✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin ’yan Kannywood da suka rasu a 2024

A cikin watanni shida da suka gabata Kannywood ta rasa jarumai hudu, mata da maza

A ranar Litinin 22 ga watan Yuli, 2024 Allah Ya yi wa jarumin Kannywood Suleiman Alaqa rasuwa.

A cikin watanni shida da suka gabata an yi rashin jarumai hudu, mata da maza a Kannywood.

Ga jerin jaruman masana’antar da suka rasu a 2024:

1- Bintu Dadin Kowa: Wadda ainihin sunanta Fatima Sa’id, ta riga mu gidan gaskiya ne a ranar 11 ga Fabrairu, 2024, a sakamakon rashin lafiya.

2- Saratu Gidado Daso: Babbar jarumar da aka fi sani da Daso, a ranar 9 ga watan Afrilu ta rasu. Amma babu labarin jinya ko wani musabbabin rasuwarta.

3- Fati Slow Motion: Wadda tsohuwar jaruamr Kannood ce ta rasu ne a kasar Chadi, inda take aure. Fatima Slow ta kwanta dama ne a ranar 28 ga watan Mayu, 2024.

4- Sulaiman Alaqa: Shi ne jarumin masana’antar na farko da aka rasa a 2024. Shi kuma a ranar 22 ga watan Yuli 2024, ya koma ga Mahaliccinsa bayan gajeruwar jinya.