✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 4 ke hana matan Kannywood zaman aure —Hauwa Rijau

Jarumar fim din Kwana Casa'in ta bayyana manyan abubuwan da ke hana matan Kannywood zaman aure

Jaruma a fim din Kwana Casa’in da Gidan Badamasi da Marainiya, Hauwa Abubakar Rijau, ainihin dalilan da ke hana matan Kannywood zaman aure.

A wata hira ta musamman da Aminiya ta yi da ita, Hauwa, wadda aka fi sani da Princess Rijau a Kannywood, ta bayyana manyan dalilai hudu da ke hana auren matan Kannywood yin ƙarko.

1- Rashin Kuɗi

Ta shaida wa wakilinmu cewa rashin kuɗi a yayin zaman aure ke sa wasu matan masana’antar fitowa daga gidan miji su dawo harkar fim.

Ta ce wasu matan Kannywood kan fito daga gidan miji ne idan bayan aure suka ga “irin yadda suke samun kudi a da yanzu ba za su ci gaba da samu ba, sai su fito su ci gaba da harkar [fim].”

Princess Rijau a Kannywood ta kara da cewa, yawancin masu auren matan Kannywood auren sha’awa ko auren jari suke musu.

2- Auren Jari

Ta ce, yawancin masu zuwa auren ’yan Kannywood, “suna mana kallon wasu mutane ne da suka tara dukiya, bari mu zo mu aure su mu ci dukiya.

3- Auren Sha’awa

“Wasu kuna suna mana aure ne na sha’awa, da zarar sun kawar da wannan sha’awa, za ka ga suna neman hanyar da za a yi a rabu.”

4- Tsangwama

Jidda Rijau ta kara da cewa matsalar yadda surukai ke daukar ’yan Kannywood na daga cikin dalilan rashin ƙarkon auren ’yan masana’antar.

“Wasu kuma kalubale ne na ’yan uwa da za su tsangwame wanda ya aure ki din, ko ke su tsangwame ki, magana daya biyu [su ce] ‘ai wannan ’yar fim’ [ce].

“Ko kuskure kaɗan kika yi su ce ai dama ’yar fim ce fa. Wannan sai ka ga ya ɗan tunzura mu, mun rabu,” in ji ta.

‘Kan-ta-waye gaskiya ne’

Jidda wadda ta fito a matsayin Hajiya Ruƙayya a fim din Marainiya, ta ƙara da cewa tabbas ana yi wa jarumai kan-ta-waye a masana’antar.

Ta kara daga cewa daga jarumai  maza da mata babu jinsin da ya tsira daga masu wannan muguwar hanya.

“Gaskiya ne ana yin kan-ta-waye, maza a yi musu na kudi, mata kuma yi musu na jikinsu,” in ji Hauwa.

Kan-ta-waye wata dabi’a ce ta damfara da ake wa sabon shiga, inda ake raba shi da wani abu.

Sai dai Hauwa Rijau ta bayyana cewa, duk da cewa akwai jarumai da masu shirya shiri da ke da wannan muguwar dadi’a ba a taru an zama daya ba.

Amma ta ce akwai kuma masu shiga rigar manyan jarumai da Daraktoci da furodusoshi su yi wa masu son shiga masana’antar Kannywood kan-ta-waye.