✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jaruman Kannywood 7 da shirin ‘Labarina’ ya haska tauraronsu

Jaruman Kannywood da likafarsu ta daga bayan fitowarsu a shirin Labarina.

Jaruman Kannywood da dama sun jima ana damwa da su a masana’antar, amma tauraronsu bai haska ba sai da suka fito a cikin shirin nan mai dogon zango na ‘Labarina’, wanda kamfanin Saira Movies ya shirya.

Ga mutum bakwai daga cikinsu:

  1. Nuhu Abdullahi:

An dade ana damawa da Nuhu a Kannywood kuma yana daga cikin matasa masu matasowa.

Sai dai kuma tauraronsa bai haska ba sai bayan da ya fito a cikin shirin ‘Labarina’ a matsayin ‘Mahmud’ kuma ya taka muhimmiyar rawa a cikin shirin.

  1. Isa Adam Feroskan:

Sunan Isa ya yi fice a wajen masu kallon fina-finan Hausa, musamman masu dogon zango.

Jarumin ya fito a cikin shirin ‘Labarina’ a matsayin ‘Presdo’ kuma ya taka rawar da ta sa likafarsa ta kara dagawa fiye da shekarun da ya shafe a baya.

 

  1. Maryam Waziri:

Tauraron Maryam Waziri ya haska, har ta zama shahararriya, bayan fitowarta a cikin fim din ‘Labarina’.

Jarumar ta yi kokari sosai a rawar da taka a cikin shirin, inda ta fito a matsayin ‘Laila’.

  1. Abdallah Amdaz:

Abdullahi, wanda aka fi sani da Amdaz, mawaki ne, marubuci kuma jarumin fina-finan Hausa da Turanci.

Amma dai bai yi fice ba kamar sauran jaruman Kannywood, sai da ya fito a cikin shirin ‘Labarina’, a matsayin ‘Excellency’.

Tabbas rawar da ya taka ta kayatar da masu kallo, wanda hakan ya sa ya zama abun burgewa musamman ga masu kallon shirin.

  1. Yusuf Saseen:

Duk da cewa jarumin bai jima ba a masana’antar Kannywood, amma ina iya cewa ya shige da ta da kafar dama bayan ya samu damar fitowa a cikin shirin ‘Labarina’.

Jarumin ya taka rawa mai kayatarwa a cikin shirin ya sa shi yin tashe da kuma soyuwa ga masu kallon shirin.

 

  1. Teemah Yola:

Fatima Isah wadda aka fi sani da Teemah Yola, ta taka muhimmayar rawa tun daga farko shirin ‘Labarina’, inda ta dinga tashi fadi da jarumar da aka shirya labarin shirin a kanta (Sumayya).

Tauraron Teemah ya haska ne saboda yadda ta dinga taimakon Sumayya wajen tsage gaskiya da kokarin dora ta kan hanya ta gari.

 

  1. Ibrahim Bala:

Wannan furodusa kuma darakta na daga cikin jaruman Kannywood, amma bai yi fice sosai da za a ce mutane da dama suka san shi.

Amma fitowarsa a cikin shirin ‘Labarina’ ya daga alkadarinsa matuka.

Jarumin ya yi kokari matuka a rawar da ya taka a cikin shirin, wanda ya fito a matsayin abokin Mahmud.