✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daina yi mana kuɗin goro — Jarumar Kannywood

Jarumar ta koka kan yadda mutanen gari ke musu kallon mutanen banza.

Jaruma a Masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Hassana Aminu, wadda aka fi sani da Hassanan Matawalle, ta ce bai kamata ake musu kuɗin goro ba.

Daga cikin fina-finan da ta taka rawa a ciki, akwai A Duniya da Gidan Danja da Dan Jarida da sauransu.

Da ta ke tattaunawa da Aminiya, jarumar ta bayyana cewa, “ka san harkar tamu wasu za su ga da zarar ka zo Kannywood wato mace da zarar ta zo gani ta ke yi ko kuma nan da kin shigo Kannywood za ki yi kuɗi ne.

“To matan da ba su shigo Kannywood ba waɗannan abubuwan suke kwaɗayi. Sai sun shigo sai su ga ashe abin da suke tunani ba haka ba ne.

“Ba su san cewa kowa dama can tana da sana’ar da tanke yi ba.

“Garin irin wannan kwaɗayin ne, idan ba a dace ba, sai ka ga yarinya ta koma zuwa gidan Gala ko su koma rayuwar otal ko ma kama ɗaki.

“Duk irin abubuwan nan ne da zarar ɗaya daga cikinsu ta yi laifi sai a yi mana kuɗin goro, a ce matan Kannywood haka suke alhali yawancinsu ma ko rajista da Kannywood ɗin ba su yi ba, amma sai ka ji ana cewa ai ’yar fim ce.”

Jarumar ta ƙara da cewa, wasu ba sa musu adalci, inda tamkar neman laifin ’yan fim ake yi.

Kazalika, ta ce da zarar an ga wata ta yi laifi, sai a fara magana, maimakon a yi musu gyara ko a yi musu uzuri.

Ƙarshe jarumar ta yi kira ga masu ɓata musu suna da cewa, su ji tsoron Allah.

Sannan ta shawarce su da su rungumi sana’a idan suna son su haɗa da harkar ta fim domin a cewarta, fim ba wurin da za a zo a yi kuɗi nan take ba ne.

“Irin su Rahama Sadau ai sana’a ta ke da ita, ita ta riƙe gam-gam kamar yadda ni ma nake da tawa sana’ar, don haka masu rara gefe da sunan fim suna ɓata mana suna, su ji tsoron Allah su gyara.”