✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jarumai mata 5 da suka taba yin aure kafin shiga Kannywood

Wasu na ganin ra zarar jaruma ta yi aure tauraronta ya kan disashe.

Akwai wasu jerin jarumai mata da sai bayan mutuwar aurensu tauraruwarsu ta fara haskawa a masanaantar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood. 

Wasu na ganin cewar da zarar jaruma ta yi aure shikenan tauraronta ya daina haske ko an daina damawa da ita a masana’antar, amma Aminiya ta yi duba a kan wasu jarumai biyar da suka shahara bayan rabuwa da mazajensu.

  1. Solskjaer ya tsawaita kwantaraginsa a Manchester United
  2. ’Yan bindiga sun yi awon gaba da takardun jarabawar NECO a Kaduna

1.Jamila Umar Nagudu

Jaruma Jamila Nagudu, ta yi fice sosai a fina-finan Kannywood, ta inda ta yi fina-finai da dama, amma kafin shigarta Kannywood ta taba yin aure har da yaro guda daya.

Jamila ta fito a fina-finai da dama amma wanda ta fi taka muhimmiyar rawa a ciki kuma wanda ya zama shi ne silar daukakarta shi ne fim din ‘Jamila da Jamilu’, wanda ta fito tare da jarumi Ibrahim Maishinku a shekara ta 2008.

Jaruma Jamila Umar Nagudu tare da danta

2. Hafsat Idris (Barauniya)

Hafsat Idris ta yi fice a masana’antar shirya fina-finai ta Hausa, bayan rabuwar aurenta da mijinta Alhaji Kabir, wanda suka haifi yara biyar da shi.

Jarumar ta fara fitowa a cikin fim din ‘Barauniya’ wanda da shi ne wasu ’yan kallo ke mata lakabi.

Tuni Hafsat ta zama daya daga cikin manyan jarumai mata kuma mai shirya fina-finai da ake damawa da su a Kannywood.

Jaruma Hafsat Idris tare sa mahaifiyarta da wasu ’ya’yanta mata

3.Umma Shehu

Umma Shehu na daya daga cikin jarumai mata fitattu a Kannywood kuma wanda suke haskawa a duniyar fina-finan Hausa.

Amma kafin shigarta masana’antar, jarumar ta taba yin aure, inda ta ke da yara mata guda biyu.

Ta fito a fina-finai irinsu Mijin Badariyya, Bakon Yanayi, Amaryar Kauye, Burin So, da kuma shiri mai dogon zango na Gidan Badamasi.

Jaruma Umma Shehu

4. Maimuna Garba (Momee Gombe)

Bayan rabuwarta da mawaki Adamu Fasaha, Maimuna Garba, wadda aka fi sani da Momee Gombe ta tsunduma cikin harkokin wakoki a masana’antar Kannywood wanda ta yi fice a cikin wakar ‘Jaruma’ ta mawaki Hamisu Breaker.

Bayan tauraronta ya haska a fagen waka, jarumar ta fara fitowa a cikin fina-finai kamar su Zainabu Abu, Manyan Mata, Gidan Danja da sauransu.

Jaruma Momee Gombe

5. Aisha Najamu

Binciken Aminiya ya gano jarumar ta taba yin aure har da yara biyu kafin ta shigo masana’antar Kannywood.

Jarumar ta yi fice a cikin shirin fim mai dogon zango na Izzar So wanda a cikinsa ne ta nuna bajinta har tauraronta ya haska, aka fara damawa da ita a cikin masana’antar.

Aisha Izzar So tare da danta

Wadannan su ne jerin jarumai mata biyar fitattu da tauraruwarsu ta fara haskawa a Kannywood bayan fitowa daga gidajen aurensu.