A fadin Ifirikiyya
Jahilci ya zam abin kiyayya
Ilmu muke nuna wa soyayya
Masana ai ta gogayya
Ko mun bar adawa da hamayya
Koyi ka koyar babu jayayya
’Yan makaranta ai ladabi da biyayya
Dodon Dodoridon duniya
Dawurwuri da duminiya
Malamai na ta hatsaniya
Tura ta kai bango
Wasu sun yi nadin damben shago
Ba sa dubin wulwulawar agogo
Uhm tsallen badaken Gizago
Dafdalar cikin kango
Duk wani mai gyara
Sai ya jure wa terere
Har da masu suka da sare-sare
Ko karo da kan kure
Bayan kuka sai an dara
Ai ta kokarin kauce wa asara
Babu tsimi ba dabara
Mai-duka yai mana sutura
Mu daina yi wa juna hantara
Domin tana sanya wasu kangara
’Yar gagara
An ce ta iya fitsara
Al’umma ta sanya mata kangara
A taimaka mata hankali ya tattara
Wahala ce tai mata makara
Kar a kira wane dan iska
Shi ma sai yai maka cin fuska
In an buga mai rauni zai sha faska
Miyagu sun washe kudin taska
Har wani yai tutiyar babban gwaska
Fitintinu sun zame mana kaska
Juhala ta saka mu tsaka
Adala muke fafutika
Jarrabawar ji a jika
Faduwar daraja ko makin daukaka
kolon malam na walgigi
’Yan dugwi-dugwi an shiga kangi
Iyaye na ta kugi
Hukuma na hargagi
Marasa kan gado na ta magagi
Can a Jihar bayan Kada
Na ga mai na-kada
Na borin kama kada
Direbobin alli a kan gada
An wancakalar da masu gada-gada
Jarrabawa ce an gwada
An gaza cin makin gina gida
An zo ana ta fada
An haifar da rudanin kida
Babu kyakkyawar ta’ada
A kwadago muna neman lada
A karo mana da la’ada
Ilmin ’ya’yanmu ya fadada
Malumma a daina kurda-kurda
Sai mu samu abin cin ragadada
Ban da tada kan adda
Ko yawan kassada
kazanta ke jawo kuda
Mu himmatu kowa ya sududa
kasarmu ta samu sa’ida
Direbobin alli
A yi aiki da hankali
Ban da kwasar albashi ai shagali
Godiyar sakarci na sukuwar dandali
Wagagen littafi da Watsattsaken fasali
Yaya za horar da Bokan Turai
Idan dan biro ya zam sakarai
’Yan dugwi-dugwi sun ga bambarakwai
Akalar aji ta zam rai-mutu kwakwai
An fasko jirginsu sarai-sarai
Gwamna el-Rusau
Abokin Malam Rubdigau
Bulalarka ba ai mata sagau
Darandakau Jikan Kwasau
Ka zama makasau
Tsaurara tsarin tsaro
Tsinin tsintsiya ya shashsharo
Kwaramniyar kwararo-kwararo
kazantar juhala an tattaro
Masu tabbatar da adala a hallaro
Saranka ya zam dubin bakin gatari
Kar a bari korarru su zam batagari
A ba su abin zaman gari
Kada al’umma ta fada garari
Mahukunta a cire mana sasari
Gwamna gwarangwam na jihar Bayan Kada ya shiga bakin duniya saboda jarrabawar ji a jika da ya aiwatar har ta jikkata direbobin alli a daukacin fadin jihar. Wannan lamari ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar nan dungurungum, har ta kai ga Dodorido ya ja bakinsa ya yi gum. Aminiyawan aminan Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya suna ta guna-guni, wai Gwamna el-Rusau abokin Malam Rubdigau ya yi wa Direbobin alli bulalar da ba a yi mata sagau. Ni kuwa na ce DARANDAkAU jikan KWASAU ka zama MAkASAU.
Batu na ingarman karfen karafan titin tarragon kwangiri, matukar Gwamnan Bayan-Kada yana sara da dubin bakin gatari, ba na tsammanin zai bar korarru, domin yana da zabi ko dai ya maishe su HORARRU ta yadda za su zama kWARARRU wajen nusar da ’yan dugwi-dugwi dimbin DABARRU don kwarewa a fannin watsattsake da buda wagagen litatttafai, ta yadda za su ji dadin baje mana ilimi a faifai; masu yada JUHALA kuwa in ba a yi sannu ba, sai an hango su da dan kamfai.
’Yan makarantar Dodorido masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya, matukar mun yarda da cewa fannonin ilimi a kasar nan na fama da jinya har ta kai ga an dade ana laluben minjirya da rawaya da za su zaburar da kuzarin al’ummar da ke fama da ciwon shawara, har su ci awara kowa ya samu warwara.
Tunda Baban-burin-huriyya ya mara wa Gwmana el-Rusau baya, kuma muna da masaniyar cewa Baba tambarin yaki da tsilli-tsillin matsalolin al’umma ne, kuma baya mai goya marayu, shi ya sa nima na bi, amma ba na son kinbibi a tsakanin masu tunkudo rawunna da kallabi; ko kiren karairayi a rambada musu zabibi, su sauya launi, har mu ci gaba da zama cikin rauni. Hattara dai al’umma. Kowa ya kara himma, a daina hauma-hauma. Watakiula wannan ne dalilin da ya nusar da Gwamna gwarangwam na Jihar Kududdufi ke yunkurin yi wa direbobin allin jiharsa JARRABAWAR JI A JIKA, don su ji dadin kamun kifi, ’ya’yanmu su ji dadin yankawa da tsitaka mai kaifi. Da sun dunsume kururrunsu, sai su ji dadin falle mujalllu da jaridu da wagagen litattafai shafi-shafi.
Lallai hakki ne da ya rataya akan kowane dan kasa nagari ya tabbatar da cewa mahukuntan Bayan-kada sun kwance mana sasari, don gudun kada a jefa al’umma cikin garari.
Gwamna gwarangwam in ka ciza, ka hura. A debi wani ba’ari na sukurkutattun direbobin alli a mayar da su zakakurai koda ba a fannin tukin alli ba, ta yadda za su zamto nagargaru, don kada su karke da zama kangararrrun kadangaru masu bula mana garu. Sauran masu hankali a kwanyarsu ku bijiro da duk wasu shawarwari da za su sanya mu kai ga gaci, don daukar tsintsiya mu share duk wata kazanta da ke yada cuta a farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen littafai, don kada juhala ta yi mana tsirara mu rika tutiya da kamfai, alhali kwanyar kwakwalen mafi yawanmu ta zama kufai.