✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jarirai 4 sun rasu a gobarar asibiti a Indiya

Iyaye na zargin jami’an asibitin sun tsere sun bar jariran bayan tashin gobarar.

Jarirai sabbin haihuwa hudu sun rasu a gobarar da ta tashi a wani asibitin yara mallakin gwamnati a daren Talata a kasar Indiya.

Iyayen jariran sun zargin jami’an asibitin da tserewa maimakon su tsaya su ceci jariran sabbin haihuwa, bayan tashin gobarar a hawa uku na benen.

Wani bidiyo da kafafen yada labaran kasar Indiya suka fitar ya nuna fusatattun iyayen jariran na zanga-zanga a harbar asibitin yara na Kamala Nehru da ke birnin Bhopal na kasar, inda gobarar ta tashi.

Ma’aikatan kashe gobara sun yi nasarar kubutar da jarirai 36 daga cikin jarirai 40 da ke dakin kwantar da jariran zuwa wani gini a asibitin.

Ministan Lardin, Vishvas Kailash Sarang, ya ce matsalar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar, wadda sai da aka shafe awa uku kafin a kashe.

Da yake ta’aziyya ga iyayen jariran, Minista Shivraj Singh Chouhan, ya sa a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin tashin gobarar.

Ya kuma sanar cewa za a biya diyyar Rupee 400,000 ga iyayen duk jaririn da aka rasa a gobarar.

Kasar dai indiya na yawan fama da matsalar tashin gobara a asibitoci.

Ko a ranar Asabar, wasu mutum 11 sun rasu bayan tashin gobara a wani asibiti a jihar Maharashtra ta kasar.