✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarirai sabbin haihuwa 10 sun mutu a gobarar asibiti a Indiya

Wasu jariran sun kone wasu kalilan kuma suka tsallake rijiya da baya

Jarirai 10 asbbin haihuwa sun mutu a wata gobarar da ta tashi ranar Asabar a wani asibitin gwamnati da ke Yammacin kasar Indiya.

Jarirai 17 ne ke sashen kula da jarirai a lokacin da gobarar ta tashi a Babban Asibitin Lardin Bhandara a Jihar Maharashtra.

Ministan Lafiya a Jihar, Rajesh Tope, ya ce uku daga cikin jariran sun kone ne kurmus, bakwai kuma sun mutu ne sakamakon hayakin da ya sarke musu numfashi.

Ya kuma bayyana cewa ma’aikatan lafiya sun yi nasarar kubutar da ragowar jarirai guda bakwai da ke bangaren.

Wani jami’in lafiya a yankin Bhandara, Prashant Uike, ya ce yaran da suka mutu ’yan kwanaki kadan da haihuwa zuwa wata uku ne.

Gwamantin Indiya ta ba da umarnin a bincko musabbabin gobarar ta safiyar Asabar da kuma yanayin ingancin kula da lafiya bayan haihuwa.

Ministan ya ce, rahoton farko-farkon da aka samu na nuna gobarar da ta tashi ne fara ne daga wata kwalabar sanya jariyar da ta kama da wuta.

“Ma’aikata sun ce cikin kankanen lokaci dakin ya turnuke da bakin hayaki,” inji shi.

Gwamnatin kasar dai ta damka wa iyaye jariran gawarwakinsu, inda za ta biya kowannensu diyydar Rupee 500,000 (kimanin dala 6,800).