✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jarabawar WAEC: Dalibai mata takwas sun kamu da COVID-19

Kawo yanzu dalibai tara ne aka gano suna da cutar, takwas daga cikinsu a Jihar Gombe

Dalibai mata bakwai da ke rubuta jarabawar sakandare ta WAEC a Jihar Gombe sun kamu da cutar COVID-19.

Kwamishinan Ilimin Jihar Gombe, Dakta Habu Dahiru ya sanar da haka, bayan wani dalibi da ke rubuta jarabawar a Jihar ya kamu da cutar.

Kwamishinan ya ce samun dalibai bakwan da cutar a Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta GGSS Doma ya sa yawan dalibai masu ita karuwa zuwa takwas.

Aminiya ta kuma kawo rahoton wata dalibai ‘yar shekara 16 mai COVID-19 da ke rubuta jarabawar daga cibiyar killace masu cutar a garin Ilorin na Jihar Kwara.