Dalibai mata bakwai da ke rubuta jarabawar sakandare ta WAEC a Jihar Gombe sun kamu da cutar COVID-19.
Kwamishinan Ilimin Jihar Gombe, Dakta Habu Dahiru ya sanar da haka, bayan wani dalibi da ke rubuta jarabawar a Jihar ya kamu da cutar.
Kwamishinan ya ce samun dalibai bakwan da cutar a Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta GGSS Doma ya sa yawan dalibai masu ita karuwa zuwa takwas.
Aminiya ta kuma kawo rahoton wata dalibai ‘yar shekara 16 mai COVID-19 da ke rubuta jarabawar daga cibiyar killace masu cutar a garin Ilorin na Jihar Kwara.
- Daliba na rubuta jarabawar WEAC a cibiyar COVID-19.
- Dalibi mai COVID-19 zai rubuta jarabawar WAEC a makaranta.
Kakakin kwamitin yaki da cutar na Jihar Kwara, Rafiu Ajakaye ya ce dalibar ta rubuta jabawar Kimiyyar Noma a ranar Laraba, karkashin sa idon jami’an jarabawar ta WAEC.
Shugabar tawagar lura da masu cutar a jihar, Dakta Kudirat Oladeji-Lambe ta ce alamun cutar ba su bayyana a jikin dalibar ba domin tana cikin mutanen da cutar ba ta nunawa a jikinsu.
“Mara lafiyar na daga cikin daliban ajin karshe na sakandare da suka yi rajistar jarabawar WAEC da ke gudana a yanzu, wanda take rubutawa daga nan. Babu wata alamar illa da cutar ta yi mata”.
Dakta Kudirat ta kara da cewa dalibar “Ta harbu ne bayan ta samu kusanci da mai dauke da cutar a cikin danginta”.
Ko kafin nan mun kawo muku rahoton dalibin farko da aka sanar yana dauke da cutar COVID-19 daga cikin masu rubuta jarabawar kammala sakandare a Jihar Gombe.