✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Janyewar Biden: Amurka ta buɗe sabon babi kan zaɓe

A yanzu dai babu wanda ke da tabbas kan abin da zai faru.

Janyewa daga takara da Shugaban Amurka Mista Joe Biden ya yi daga zaben da za a yi a watan Nuwamban bana ya sa kallo ya koma sama game da babban zaɓen ƙasar.

Bayan kwashe makonni Shugaba Biden yana turjiya tare da kafewa a kan lallai zai tsaya wa Jam’iyyar Democrats takara, a zaben Nuwamban bana sai ga shi a ranar Lahadin da ta gabata Shugaban ya yi ribas inda ya bayyana cewa ya janye niyyarsa ta tsayawa takarar.

Kafar labarai ta BBC Hausa ta bayyana tasirin da ake tunanin wannan mataki zai yi a kan manyan masu ruwa-da-tsaki a zaɓen: Wato Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris da Jam’iyyar Democrats da kuma Donald Trump.

Ganganci ne tsayar da Kamala Harris amma ’yan Democrat da yawa na son haka.

Niyyar da Shugaba Biden ya bayyana ta mara wa Kamala Harris baya ya ƙara ƙarfafa yiwuwar ta samu tikitin tsayawa takarar Shugaban Kasar.

Ya ce zai ba ta goyon baya ɗari bisa ɗari, tare da bayyana zaɓen da ya yi mata a matsayin Mataimakiyarsa shekara huɗu da suka gabata a matsayin mafi kyawun zaɓi a rayuwarsa.

Akwai yiwuwar cewa ’ya’yan Jam’iyyar Democrats da dama za su bi zaɓin Shugaban Kasar domin gudun yin wani abu za zai ƙara dagula al’amura yayin da suke da ƙasa da wata guda kafin babban taron jam’iyyar na ƙasa.

Mataimakiyar Shugaban Kamala Harris – na ci gaba da samun tagomashi a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar na ta maye gurbin Mista Biden.

A matsayinta na Mataimakiyarsa, ta zama jagorar yaƙin neman zaɓen gwamnati, musamman a makonnin bayabayan nan.

Manyan ’ya’yan Jam’iyyar Democrats a Amurka na ci gaba da nuna goyon bayansu ga gare ta a matsayin ’yar takara bayan janyewar Shugaba Biden daga takarar.

Gwamnan Jihar Kalifoniya Gavin Newsom da ake ganin yana ɗaya daga cikin wadanda za su fito su kalubalance ta a takarar ya sanar da mara mata baya, yana mai bayyana ta a matsayin marar tsoro.

Tun farko Kamala Harris ta gode wa goyon bayan da Shugaba Biden ya ba ta, inda ta bayyana matakinsa na janyewa a matsayin kishin ƙasa da rashin fifita bukatun kashin kai.

Tuni gwamnoni uku da sanatoci takwas da ’yan Majalisar Wakilai suka sanar da goya mata baya. Haka ma tsohon Shugaban Kasar Bill Clinton da matarsa Hillary Clinton da wasu mashahuran ’yan fim da mawaka na Hollywood sun ce suna tare da ita.

Sunan Kamala Harris ya ƙara fitowa fili ne a lokacin da Biden ya zaɓe ta a matsayin Mataimakiyarsa, sai dai ta yi fama da ƙarancin ayyuka a lokacin mulkin.

Kashi 51 na Amurkawa ba sa goyon bayan Kamala Harris, yayin da kashi 37 ke goyon bayanta, kamar yadda alƙaluman ƙuria’r jin ra’ayin jama’a da Five Thirty Eight ta gudanar ta nuna. Akwai dalilai da dama da za su sanya hakan.

Bisa ƙa’idar Kundin Tsarin Mulki ita ce ta farko a jerin waɗanda za su iya gadon Shugaban Kasar.

Amma miƙa ragamar yin takarar shugabancin ƙasa ga mace baƙar fata zai iya zama gurguwar shawara.

Kuma da zarar aka yi hakan za ta kasance ɗaya daga cikin masu juya kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe kimanin Dala miliyan 100 da aka tara zuwa yanzu.

Mene ne hadɗuran?

Ra’ayin jama’a ya nuna cewa Kamala Harris ba ta da farin jini sosai, kamar shi Biden kansa.

Kuma idan aka kwatanta ta da Donald Trump, kusan kamar yadda suke ne da Shugaba Biden.

Abu na biyu shi ne Kamala Harris ta samu tangarɗa a muƙaminta na Mataimakiyar Shugaban Kasa.

A farkon wa’adin mulkinsu an ɗora mata nauyin magance matsalar ’yan ci-rani da ke shiga Amurka ta kan iyaka da Meziko.

Wannan ya kasance gagarumin aiki a kanta, kuma wasu kura-kurai da aka samu da wasu kalamai da ta furta sun janyo mata suka.

Kuma ita ce mai kula da batun ’yancin zubar da ciki na gwamnatin, wanda wani lamari ne da ta yi ƙoƙari a wannan fanni.

To amma abubuwan da suka faru tun farko ba za a manta da su ba.

Abu na ƙarshe shi ne – Kamala Harris ta taɓa yunƙurin tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2020, inda ta yi mummunan shan kaye.

Tsayar da Kamala a yanzu abu ne mai cike da haɗari sai dai kuma babu wata hanya mai sauƙi a yanzu.

Kuma yiwuwar samun nasarar Donald Trump a zaɓen na ci gaba da kara ƙarfi.

Za a iya samun hatsaniya a lokacin babban taron Democrats

Shekaru masu dama da suka gabata, babban taron jam’iyyun Amurka kan zamo lami.

Babban taron Jam’iyyar Republican da aka gudanar a makon jiya, inda a lokacin aka tsayar da Donald Trump shi ma haka ya wakana.

To amma da alama babban taron Jam’iyyar Democrats da zai gudana nan da wata ɗaya mai zuwa a Chicago zai sha bamban.

Koda kuwa Jam’iyyar Democrats ta yanke sahwarar mara wa Kamala Harris baya, zai yi wahala ta cim ma nasarar yin yadda ta so baki ɗaya.

Kuma idan Kamala ta kasa haɗa kan jam’iyyar, to kuwa taron zai zamo babu tabbas.

Zai zamo babban taron jam’iyya wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihi.

An rikirkita shirin ’yan Republican

An tsara babban taron Jam’iyyar Republican na bana ne ta yadda babban abin da zai fi mayar da hankali shi ne tallata manufofin jam’iyyar da kuma sukar mutum ɗaya tilo, wato Shugaba Biden.

Sai dai yanzu da Biden ya yi watsi da batun takararsa, ya rikirkita wa Trump da muƙarrabansa shirinsu baki ɗaya.

Taron ya yi ƙoƙarin bayyana ɗan takarar Republican a matsayin jarumi, hatta shigowarsa wurin taron ma abin kallo ne, gabanin shigowar fitaccen ɗan wasan damben nan na duniya Hulk Hogan.

A bayyana take yadda aka so a fito da Trump a matsayin jarumi tare da kwatanta Biden a matsayin mai rauni.

To amma duk yadda za ta kasance a yanzu ɗan takarar Democrats zai zamo mutum ne mai ƙarancin shekaru fiye da na Shugaban Kasar.

Saboda haka kwatanta Trump a matsayin mai kuzari da Kamala ko wani daga cikin ’yan takarar Democrats a yanzu ba zai yi aiki ba.

Idan Kamala ta zama ’yar takarar Shugaban Kasa, to tabbas ’yan Jam’iyyar Republican za su yi ƙoƙarin yin amfani da abubuwan da ake kallo gazawa ne na gwamnati mai ci wajen sukarta.

Sannan duk wanda Jam’iyyar Democrats ta tsayar, babu shakka ’yan Jam’iyyar Republican za su zarge shi da hannu a yin rufa-rufa kan gazawar Biden sanadiyyar tsufa da kuma cewa sun saka ƙasar cikin haɗari.

A yanzu dai babu wanda ke da tabbas kan abin da zai faru.