Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in dan yi tsokaci a kan wata raguwar dabara da na ji gwamnatin Najeriya tana kokarin yi ta janye sojoji daga yankunan da ayyukan ’yan ta’adda suka yi sauki.
To a gaskiya wannan kuskure ne, mai wuyar cike gibi, wanda nake gani kamar zai fi kuskuren baya, lura da cewa su kansu sojojin ma yaya aka kare balle a ce za a sakar wa ’yan sanda da Sibil Defens da kuma ’yan banga ko ’yan kato da gora kula da yankunan ? Ni dai a gaskiya ba na goyon bayan haka, domin kuwa har yanzu ’yan Boko Haram suna da karfi a wasu yankunan Jihar Borno da Yobe. Da gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da shawarata maimakon janye sojojin da kokarin kara sojojin ta yi, domin dan hakkin da ka raina shi ne zai tsone maka idanu. Tunda ana ganin an ci karfinsu mai zai hana a kara yawan sojojin don karasa murkushe su baki daya. Gyara kayanka dai ba zai zama sauke mu raba ba.
Daga Ashiru Usman Sabuwar Gwaram, 07030817573.
Murnar shiga shekarar 2020
Assalam Aminiya,. Ina yi muku barka da shiga sabuwar shekara ta 2020. Allah Ya sada mu da alherinta Ya ba mu lafiya da zaman lafiya a duniya baki daya, amin.
Daga Alhaji Umar Foreba Gashuwa. 08108003333.
Fatar alheri ga Aminiya
Assalamu alaikum Edita. Jinjina ga Kamfanin Media Trust, mamallakin jaridar Aminiya da Daily Trust. Ganin irin yadda wannan kamfanin jarida yake fadakar da al’umma gami da nishadantarwa da ilimamtarwa. Ni ba bako ne wajen karanta jaridar Aminiya ba, ina muku jinjina gami da fatar alheri. Allah Ya kara basira da daukaka da kuma hazaka, amin.
Daga Masoyin Jaridar Aminiya, Iliyasu Ibrahim KD, Danbushiya, Jihar Kaduna, 07016995298.
Barka da Sabuwar Shekarar Miladiyya
Salam zan yi amfani da wannan dama domin in mika sakon barka da sabuwar shekarar Miladiyya ga dukkan ma’aikatan wannan jarida mai albarka. Allah Ya yi muku jagora Ya kara muku kwarin gwiwa a kan aikinku. Allah Ya ba mu zaman lafiya da wadata.
Daga Nura Muhammad Mai Apple, Gusau. [email protected]
Godiya ga Aminu Jamu Daura
Assalam Edita. Ina so ka ba ni dama domin in kara yin godiya ga Hon. Aminu Jamu Daura, saboda irin abin arzikin da ya yi mini. Shi ne mutum na biyu a duniya wanda har in koma ga Allah ba zan taba mantawa da su ba. Na farko tsohon Shugaban Hukumar Ilimi Bai-Daya ta Jihar Katsina Alhaji Aminu Danbaba Khadimul Islam na Masarautar Daura, wanda shi ne ya dauke ni aikin gwamnati. Sai Alhaji Aminu Jamu, wanda ya biya mini makudan kudi aka yi mini tiyata a asibitin Bawo Clinic Daura. Don haka ina fata Allah Ya kara kare shi daga sharrin abokan halitta mutum ko aljan, amin.
Daga Hadi Tsohon Sarki Daura 07015256836
Kira ga Gwamnatin Kano
Assalam Edita. Da fatar kana lafiya. Tabbas kauyukan Karamar Hukumar Tofa na cikin lahaula, ba hanya, ba ruwa, ba wutar lantarki, ba wani aikin ci gaban da ake yi mana.
Daga Y. Yarimawa, 08056333326.
Taya murnar cika shekara 63
Assalam AMINIYA yaya aiki? Ina mika sakon taya murnar cika shekara 63 ga Mai girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, baya goya marayu, jigon talakawa. Sannan muna yi wa Abba Gida-Gida fatan Allah Ya yi wa rayuwa albarka tare da kara nisan kwana.
Daga A’isha Muhammad Gombe. 07087675948.
Hadarin mota: Sakon ta’aziyya
Assalam Edita. Ya Allah muna tawasali da tsarkakan sunayenka 99 Ka jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota a garin Gozaki a Jihar Bauchi. Allah Ya sa Jannatul Firdausi ce makomarsu, amin.
Abu Yazyd Loko, 08075859580.
Jinjina ga Sanata Kabiru Gaya
Edita a taimaka mini in jinjina wa Sanata Kabiru Gaya da ya yi dogon tunani da ya hango daya daga cikin matsalolin kasar nan. Aikinka ya yi kyau Sanata Gaya saboda yunkurinka na a rage jam’iyyu su koma biyar kacal. Duk mai son dimokuradiyya da kasar nan zai so haka. Wani hanzari ba gudu ba shi ne a kara rage yawan ’yan majalisa na dattawa da wakilai da jihohi saboda suke zuke kudaden da suka kamata a yi wa kasa aiki.
Daga Lawan Yaro Bichi, 09023326156.
Dokar sakin aure a Kano
Assalam Edita. Mun karanta bayani a cikin Aminiya cewa za a yi doka kan sakin aure a Kano. Idan mu maza muna da laifi to yaya za a yi da matan da ke neman sai an ba su saki? Yanzu haka akwai mata da yawa da suka tafi Makkah neman kudi sama da shekara 10 suna can mece ce mafita ko makomar irinsu?
Daga A. Abdul Jigawa, 08134540157.
Idan an saki ’yan mari za a iya
sakin fursunoni
Assalam Edita. Ka ba ni dama in yi tsokaci kan sakin ’yan mari da ake yi. Hakan ba zai haifar da da mai ido ba, domin kuwa duk wanda ka gani a wurin saboda ya gagari iyayensa ne ya sa aka daure shi, ba nagari ba ne, kuma a can ana kula da tarbiyyarsa gami da addininsa. Yanzu masu laifi za su karu, barna za ta karu, gyara ya kamata a yi a kan haka, kamar abincinsu da wurin kwanansu da tsabtar muhallinsu da kula da lafiyarsu ne mafita amma ba sakinsu ba.
Daga Raheenat Kofar Mazugal Kano, 09038967985.
Tunatarwa ga Ganduje da Kwankwaso
Assalamu alaikum Edita. Ina son ka ba ni dama in roki Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Ganduje da tsohon Gwamna Sanata Rabi’u Kwakwaso don Allah don Annabi (SAW) ku daina kai ’yan uwanmu Musulmi suna kashe kansu kuna bata mana sunan Arewa.
Malam Sanda Dan Zariya, Kasuwar Mil 12 Legas, 08101619017.
Jinjina ga Adam A. Zango
Assalam Editan, jinjina zuwa ga Adam A. Zango, kamar yadda ka dauki nauyin karatun daliban makarantar nan, kai ma Ubangiji Allah Ya taimake ka Ya kare ka.
Daga 08039258288.
Matashi mai kishin talaka
Assalam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yaba wa matashin nan mai kishin talaka wato Bashir Sanata dan Jam’iyyar PDP a Jihar Kano, kuma dan amanar Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa yadda ba dare ba rana yake tsaye don ganin an tallafa wa talaka kuma an hada kai a ko’ina don a samu ci gaba. Da fatar Allah Ya kara jagora Ya ba ka ikon ci gaba da fadin gaskiya Ya kuma kawo babar kujera, amin.
Daga Musa GGC, Kurna Kano, 08038822292.
Tunatar da ’yan Arewa
Edita sannunku da aiki. So nake ka ba ni fili in ja hankalin ’yan uwana ’yan Arewa gaba dayanmu. A yanzu dan Arewa yake mulkar kasar nan, sai ga shi wadansu a Arewa na cewa bai tsinana wa Arewa komai ba, har da cewa talakawan Arewa suka zabe shi suna goranta masa. To tabbas talakawa suka dora shi kan mulkin Najeriya amma ba da son zukatan wadansu manya ba, kuma fadar hakan ruwa ne ya kare wa dan kada, wahalar da kuka bai wa talakawa ce tushen samun mulkin Buhari. Talakawa sun ga mafita suka watse muku. Gaskiya dai daci gare ta mai fadarta ba ya da farin jini ga makaryaci.
Daga Ibrahim Dankoli, Jada Adamawa, 07034542318.
Gyaran hanya
Salam Editan Aminiya. Ina son ka ba ni fili a jaridar nan, kamar yadda Auwalu Datti ya yi jinjina ga Kwamashinan Ayyuka da Gidaje Aminu Usman P A, muna so kamar yadda aka dauko aikin titi daga Kofar Gidan Sardaunan Gumel zuwa Balai Kofar Auwalu Garba muna so ta zarce zuwa layin Gidan Magaji Maye, har kan babban titi Hadeja. Da fatar za a taimaka.
Daga Rabi’u A. Usman Mailu Zuwan Wanki Gumel 07034852558.
Najeriya na bukatar mu yawaita addu’a
Assalam Edita. Ina fata kana lafiya, Allah Ya kara wa iliminka albarka. Don Allah ina so ka ba ni dama in yi kira ga al’ummar Najeriya ba mu da wata kasa da ta fi mana ita, kasarmu tana bukatar addu’a. Mu yawaita addu’a a kan Allah Ubangiji Ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa. Allah Ya kuma sanya albarka a abin da muka noma, amin.
Daga Haladu Ahmadu Chibiyayi, Zaki Jihar Bauchi. 08030703952.
Bude kasuwar garin Gaidam
Assalam Edita. Don Allah mu al’ummar garin Gaidam ka mika mana gaisuwarmu da godiya ta musamman zuwa ga Gwamnan Jihar Yobe game da wannan goma ta arziki da ya yi mana ta bude kasuwar Gaidam.
Daga Abdullahi A. Tsangaya, 09076468540.
Matsalar sace wayar wutar lantarki
Assalamu alaikum. Muna kira ga shugabannin siyasa na Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe su duba matsalar sace wayar wutar lantarki da aka yi a daya daga taransfomomin wuta na Tumu wadda ta sa yanzu wani sashin garin ba wutar lantarki. A kawo mana dauki don Allah.
Daga Isa Usman Tumu. 07060563008.
Kira ga Hukumar Ilimi ta Jihar Kano
Don Allah me hukumar ilimi take nufi da sanya farin yunifoam a makaranatar gwamnatin jihar tun a firamare zuwa sakandare abin da ke wahalar da iyayenmu wajen wanki sabanin sauran birane tun a firamare za ka gansu abin sha’awa? Misali, idan ka je Jihar Kaduna bakinka ba zai rufu ba don sha’awar da dalibai za su ba ka ganin kure hange za ka yi ta yi ba tare da gajiya ba a makarantunsu.
Daga Hafiz Na-Ma’aiki Gwarzo, 08140900999.