✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Janar din sojojin Najeriya 18 sun kamu da COVID-19

Rahotanni sun nuna cewa akasarin su sun kamu da ita ne yayin wani taron Babban Hafsan ojin Kasa na kasa na 2020.

Akalla manyan sojojin Najeriya masu matsayin Janar guda 18 ne ke fama da cutar COVID-19 bayan bincike ya tabbatar suna dauke da ita.

Rahotanni sun nuna cewa akasarin su sun kamu da ita ne yayin wani taron Babban Hafsan ojin Kasa na kasa na 2020.

Wani babban soja a Shalkwatar Sojin Kasa ya shaida wa Aminiya cewa akwai yuwuwar sun harbu da ita ne daga marigayi Manjo Janar Johnson Irefin wanda ya mutu a kwanakin baya.

“Ko tantama babu sun kamu da ita ne yayin taron wanda aka soke daga baya. Mu na addu’ar Allah ya tashi kafadunsu cikin gaggawa,” inji shi.

Majiyar ta kuma kara da cewa marigayi Janar Irefin ya ziyarci wasu abokan aikinsa kafin ya halarci wurin taron.

Daga nan ne Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta umarci dukkan sojojin da suka halarci taron, su da matansu da sauran iyalansu da su killace kansu na tsawon mako daya.