Janar guda 29 na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na gab da fara hutun barin aiki bayan nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Rundunar.
Aminiya ta gano cewa janar-janar din da za a tura hutun su ne ’yan aji na 36 a Kwalejin Kananan Hafsoshi ta NDA.
- Aminanshi sun kashe shi kan bashin da yake bin su
- ’Yan boko na neman wargaza Najeriya —Sarkin Musulmi
Manjo-Janar Farouk Yahaya dan aji na 37 ne, lamarin da ya sa ake ganin matakin a matsayin take-taken yi wa Janar-janar din ritaya.
Bisa al’adar soji, duk lokacin da aka nada wani Janar a matsayin Babban Hafsan Runduna, to a kan yi wa ’yan ajin gaba da shi ritaya.
Amma mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro, Birgediya Bernard Onyeuko ya musanta cewa akwai shirin yi wa Manjo-Janar 29 da ake magana a kansu ritaya.
Da yake jawabi a makon jiya, Birgediya Onyeuko ya ce yin ritaya abu ne na zabi ga manyan hafsoshi.
Amma a ranar Litinin Aminiya ta gano cewa ana shirin yi wa masu mukamin Manjo-Janar 29 ritaya.
Majiyarmu ta soji ta ce tuni aka sahale musu su fara hutun barin aiki da ake kira “hutun shekara”.
“Ka san dole sai Majalisar Soji ta amince da hakan, amma tunda ba ta riga ta amince ba, ba zai yiwu a sanar a hukumance ba,” a cewar majiyar.
A ranar Litinin, Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi, ya gabatar da Manjo-Janar Farouk Yahaya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Sun kuma yi wata ganawa tare da Babban Hafsan Tsaro, Laftanar-Janar Leo Irabor a Fadar Shugaban Kasar kan halin da tsaro ke ciki a Najeriya.
Bayan ganawar, Ministan Tsaro ya ba da tabbacin inganta tsaro da kuma kare rayuka da duniyoyin al’umma.