Gwamnatin Jamus ta amince da tsarin halarta tabar wiwi ga wadanda suka zarta shekaru 18 da haihuwa.
Sai dai gwamnatin ta ce tana jiran sahalewar fannin shari’a na kotun Turai a kan wannan batu domin aiwatar da shi a shekara ta 2024.
- INEC Ta Kama Ma’aikata 23 Masu Yi Wa Mutane Rajistar Bogi
- Iran ta kakaba wa wasu mambobin EU takunkumi
A wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Berlin, Ministan Kiwon Lafiya na Jamus, Karl Lauterbach ya ce wannan yana nufin cewa jama’a na iya samarwa da yin kasuwancin tabar wiwi, tare da saya ko mallakar Gram 20 har zuwa 30 na wannan taba.
A shekara ta 2024 ne dokar halarta tabar wiwi za ta fara aiki a Jamus idan komai ya tafi salin-alin.
Wannan sassaucin zai sanya Jamus zama daya daga cikin kasashen Turai da suka soke haramcin shan taba wiwi.
Burin da fadar mulki ta Berlin ta sa a gaba, shi ne tabbatar da kariya a fannin kiwon lafiya da kuma dakile laifuka da ke da nasaba da kasuwar taba wiwi ta bayan fage.