Akalla kayayyakin tarihi 7,000 ne kasar Jamus ta shirya dawowa da su Masarautar Benin da ke Jihar Edo a Najeriya, bayan shekaru da dama da kwashe su.
Tuni dai aka fara dawo da wasu daga cikin kayayyakin tarihin zuwa Najeriya.
- Kuskure ne ziyarar da Ganduje ya kai wa Garo —Kwamishina
- Badakalar N80bn: Kotu ta ba EFCC umarnin tsare Akanta-Janar na Kasa
Sai dai an sha tirka-tirka tsakanin masarautar ta Benin da kuma bangaren gwamnatin Jihar Edo kan wanda ke da alhakin karbar kayayyakin na tarihi.
Amma daga bisani an cimma matsaya tare da gabatar da tsare-tsare da za su tabbatar da cewar wadannan kayayyakin tarihi an ci gaba da adana su ba tare da sun salwanta ba.
A 2021 ne wata tawaga daga Jamus karkashin jagorancin Jakadan Najeriya a can, ta yi takanas har Fadar Sarkin na Benin, inda aka fara mika wadannan kayayyakin tarihi daga cikin kayayyakin kimamin 7,000 ga masarautar.
Tun kafin kaiwa ga tantance inda ya kamata a mika wadannan kayayyakin tarihi da Jamus din ta kwashe shekaru aru-aru, sai da aka yi ta kai ruwa rana da gwamnatin jihar, wadda ta kafe cewa ita ya kamata a bai wa, ita kuma masarautar ke ganin ta fi cancantar karbar su.
Wannan yanayi dai ya sa an kwashe kwanaki ana rawar ’yan mata, wanda da ya sa tunani ga Jamus din da ma duk masu lura da al’amuran kayan tarihi.
Amma daga bisani an cimma maslaha, inda masarautar ta karbi wadannan kayayyaki, cikin tsari da mutunci da kuma alkawarin gina dakunan ajiye su don amfanin ma su ziyara daga ciki da wajen Najeriya.
Tarihi dai ya tabbatar cewar kimanin kaso 90 cikin 100 na kayayyakin tarihi na jibge a nahiyar Afirka, sai dai turawan yawon duniya sun jide su zuwa kasashensu.