Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya ce akalla ’yan Najeriya 14,000 da ke zaune a kasarsa ne suke fuskantar barazanar a fitar da su daga kasar.
Ya ce za su dauki matakin ne saboda ƙaruwar yadda ’yan Najeriya ke neman mafaka a kasar ba tare da cikakkun takardun shaidar gane ko su su wane ne ba.
- Mun kashe wanda yake ƙera wa Hamas rokoki – Isra’ila
- An harbe shi har lahira a wurin gwajin maganin bindiga
Olaf ya kuma ce akalla ’yan Najeriya 12,500 ne suke zaune kara-zube sakamakon gwamnatin Najeriyar tana barin wadanda ba su cika ka’ida ba su bar kasar.
Da yake jawabi yayin wata tattaunawa da Shugaban Kasa Bola Tuntubi a Abuja ranar Talata, Olaf ya ce, “Karuwar yawan ’yan Najeriyar da suke neman mafaka a Jamus a 2023 ya yi tashin gwauron zabo.
“Kusan mutum 14,000 ne za mu iya mayarwa kasarsu, kuma akasarinsu ma ba su da halastattun takardun zama a kasar.
“A shirye muke mu hada gwiwa domin inganta harkokin shige da fice a tsakaninmu,” kamar yadda wata sanarwa daga Fadar Shugaban ta fada.
A wani labarin kuma, Shugaba Tinubu ya ce akwai damar ci gaba da tattaunawa domin ganin ba a kai ga dawo da su gida ba.