Gwamnatin Jamus ta ware Euro biliyan 65 domin rage wa iyalai da kamfanoni radadin tsadar makamashi da suke fuskanta a halin yanzu.
Gwamnatin ta ce ta kaddamar da sabon shirin don taimaka wa magidanta shawo kan hauhawar farashin kayayyaki.
Haka kuma, ta ce tana sa ido kan ribar da kamfanonin makamashi ke samu don taimakawa wajen samar da tallafin.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ce sun dauki matakan gaggawan ne saboda lokacin sanyin hunturu da ke gabatowa don saukaka wa al’umma samun saukin dumama gidajensu.
Sanarwar wannan aniyar dai ta zo ne bayan matakin da Rasha ta dauka na katse samar da makamashin iskar gas ta bututun nan na Nord Stream 1 wanda ke sama wa kasashen Turai makamashin.
Tsarin rage radadin karo na uku, zai hada da rage wa mutane kudin tikitin tafiye-tafiye da na wuta da iskar gas ga ’yan fansho da dalibai da ma sassauta wa kamfanoni da ke cin makamashi sosai.
Yanzu haka ’yan kasuwa da masu saye a Jamus na jin radadin tsadar makamashi da ya yi mummunan tashi, yayin da kasar mafi girman tattalin arzikin a Turai ke neman hanyoyin janye kanta daga dogaro da kayayyakin Rasha sakamakon mamayar da ta yi wa Ukraine.
Watanni ukun da suka gabata ne dai gwamnatin Jamus din ta sanar da rangwamen tikitin zirga-zirga zuwa ko’ina na kasar zuwa euro tara a wata.
Yanzu kasar ta kintsa wa samar da wadatacciyar gas da mutane za su iya amfani da ita lokacin sanyi na hunturu da ke tafe, domin kauce wa yankewar wuta da ayyukan na’urorin dumama gidaje da wuraren aiki.