Kasar Ukraine ta zarti Jamus da yin biris da rokonta na ba ta tankokin yaki samfurin ‘Leopard’ da za su taimaka mata sosai a yakin da take ta ke yi da Rasha.
Ministan Harkokin Waje na Ukraine, Dmytro Kuleba ne ya bayyana haka, yana mai cewa, “maimakon su share man hawaye sai wasu uzururruka suke bamu marasa ma’ana”.
- Yakin Ukraine zai kawo koma baya ga tattalin arzikin duniya – Bankin Duniya
- Shekara 31 da samun ’yanci: Yadda yakin Rasha ya raba kan ’yan Ukraine
Ministan ya ce, Ukraine na bukatar tankunan yakin ne domin ta kwaci ’yan kasarta daga danniya da kuma kisan kare-dangi na Rasha, yayin da sojojinta ke kutsa kai cikin yankin Kudancin kasar domin kwato wuraren da Rasha ta mamaye.
Ministar Tsaron Jamus, Christine Lambrecht a ranar Litinin, ta sake bayyana kin bukatar da Ukraine ta gabatarwa da kasarta.
Ministar ya ce, “Babu wata kasa ta Turai da ta ba Ukraine tankar yakin da ta kera ta gani-ta-fada, har yanzu. Mun kuma yi yarjejeniya da abokanmu na cewa ba za mu yi gaban kanmu ba, sai mun tuntube su [kan wannan lamari]” In ji Ministar Jamus.
Kasar Ukraine ta karbi tankunan yaki 230 kirar kasashen da ke karkshin yarjejeniyar Warsaw, daga Poland da kuma Czech tun lokcin da Puttin ya mamayi kasar a ranar 24 ga watan Fabarairu.
Kasar Biritaniya kuwa, ta ba ba Ukraine motoci masu silke 120, ciki har da motocin sintiri na kirar ‘Mastiff’ na musamman, sannan ta ba ta dubban harsashen tarwatsa tankunan yaki.
Kasar ta kuma ba Ukraine jirage masu sarrafa kansu, da kuma a kalla makaman harba rokoki kirar M270 uku.
Amurka ita ta fi bayar da gudunmwa ma fi yawa na tallafin da ya kai kimanin Dala biliyan 8.79 g ga Ukraine don ta samu nasara a kan Rasha.
An yi amanna da cewa, wadannan gudunmawa na makamai da kasahen yamma su ka ba Ukraine ce, ta ba ta nasarar cin galaba kan Rasha a kudancin Kherson da kuma arewa muso kudu na Kharkiv a ‘yan kwanakin nan.