✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyun Najeriya ba su da akida ko manufa – Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai, Barista Yakubu Dogara ya ce jami’iyyun siyasar kasar nan, ba su da karfi kuma a rikice suke kuma ba su da tsarin…

Shugaban Majalisar Wakilai, Barista Yakubu Dogara ya ce jami’iyyun siyasar kasar nan, ba su da karfi kuma a rikice suke kuma ba su da tsarin jam’iyyar siyasa mai kazar-kazar sannan suna fama da rashin kintsi da dimokuradiyyar cikin gida.

Shugaban Majalisar ya bayyana haka ne a a ranar Litinin lokacin da yake bude taron fadakarwa na wuni biyu da Cibiyra Harkokin Shugabancin Jam’iyyun Siyasa da Bunkasa Tsare-Tsare (PPLPDC) ta Cibiyar Tsare-Tsare da Dabarun Bunkasa kasa ta kasa (NIPPS) da ke Kuru a Jos ta shirya a Abuja.

Taron mai taken: “Ingantacciyar Hanyar Tafiyar da Jam’iyyun Siyasa Cikin kwarewa,” Dogara ya ce magudin siyasa ce ga duk wani zababben jami’in gwamnatin ya yi shugabanci ba tare da yana bin manufofin da jam’iyya ta gabatar ga masu zabe ba, wadanda kuma su ne suka sa aka zabe su.

Honorabul Dogara wanda Mai tsawatarwa na Marasa Rinjaye Honorabul Yakubu Umar Barde ya wakilta ya ce wajibi ne jam’iyyun siyasa su rika dogaro da manufofinsu domin tsara dabarun yin ayyuka da za su kawo ci gaban kasa.

 Ya ce raunanan jam’iyyu ba za su karfafa dimokuradiyya, kuma a matsayinsu na jam’iyyun siyasa ana sa ran su yi dimbin ayyuka ciki har da kawo kyakkyawan shugabanci.

 “Idan jam’iyyun siyasa suna son su taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da mulkin dimokuradiyya, wajibi ne su gudanar tare da aiwatar da abubuwan da za su gina amana a tsakani masu zabe. A Afirka musamman a Najeriya, jam’iyyun siyasa suna da rauni, babu kintsattsiya kuma jam’iyya mai kazar-kazar kuma ba su da armashi a wurin jama’a,” inji Dogara.

Ya kara da cewa: “Wadannan raunanan jam’iyyu ba za su iya karfafa dimokuradiyya ba, a matsayinsu na jam’iyyun siyasa ana sa ran su gudanar da muhimman abubuwa da suka hada da wayar da kan jama’a da sanya musu sha’awa da tsara harkokin jama’a da horar da shugabanni da kuma tsara gwamnati.”

Ya lissafo matsalolin da suke addabar daidaikun jam’iyyun, inda ya ce, sun hada da rashin gamammn tsari da binciken da ya ginu a kan manufar hanyoyin bunkasawa da za su samar da fitaccen tsari kan yadda za su gudanar da shugabanci, sai rashin akida ko abubuwan da suka ginu a kai da karancin gogewa a fagen bincike da nazari da za su auna rawar da suka taka da kuma fitattun tsare-tsare da dabarun gina jam’iyya.

 “Yana da muhimmanci mu tsara jam’iyyunmu a kan gwadaben gudanar da harkokin mulki yadda ya kamata da kafa tsare-tsaren da za su tafiyar da ayyuka tare da samo kwararru su gudanar da bangarorin mulki na jam’iyyu, sannan mu bayar da goyon baya ga shugabannin jam’iyyar da suke gudanar da jam’iyyunmu,” inji shi.