Ma’aikatan jami’o’i sun fara yakin aiki domin matsa wa gwamnati lamba ta biya musu bukatunsu.
Yajin aikin na kwana 14 na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shirye bude jami’o’i domin ci gaba da darussa.
Kungiyoyin manyan ma’aikata da wadanda ba malaman jami’o’i ba (SSANU da NASUU) sun fara yajin aikin ne daga Litinin 5 ga Oktoba, 2020.
Ma’aikatan na zargin bambance-bambance a tsarin albashin bai-daya (IPPIS) da kuma rashin biyan su alawus-alawus dinsu.
Shugaban SSANU, Kwmaret Samson Ugokwe, ya kuma zargin malaman jami’o’i da kwace shugabancin bangarorin da ba na koyarwa ba.
Ya ce yin hakan “ya saba ƙarara da tsarin aiki da kuma dokokin da suka kafa bangarorin”.
Sauran bukatun sun hada da biyan su alawus-alawus din da ma’aikatan suka cancanta da kuma magance almundahana a jami’o’i.