Wani jami’in soja ya yi batan dabo jim-kadan da harin ’yan bindiga kan Sansanin Soji dake yankin Zazzaga na Karamar Hukumar Munya ta jihar Neja.
Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun kaiwa sojojin farmaki ne a sansaninsu inda suka kwashe kimanin sa’o’i biyu suna ta musayar wuta da su.
- Buhari ya sake nada Jelani Aliyu a matsayin shugaban NADDC
- Danganta Pantami da ta’addanci zalunci ne —Izala
- Ba mu tattauna batun Pantami a taron Majalisar Zartarwa ba – Lai Mohammed
Wata majiya ta ce an raunata ’yan bindigar da dama, ko da dai Aminiya bata da tabbaci a kan hakan.
A hari na baya-bayan nan da aka kai jihar kimanin makonni uku da suka wuce shi ne wanda wata tawagar ’yan bindiga masu tarin yawa suka kai wani sansanin jami’an tsaron hadin gwiwa dake Allawa da Basa dake Karamar Hukumar Shiroro ta jihar , inda suka yi wa wasu sojoji biyar da wani dan sanda kisan gilla.
Duk da cewa babu wani rahoto da yake nuna an kashe Soja ko da guda daya a wannan sabon harin, Rundunar Sojin ta bayyana bacewar jami’inta guda daya.
Aminiya ta rawaito cewa, ’yan bindigar sun kutsa cikin yankin Zazzaga da misalin 4:00 na dare, inda suka rarraba kansu zuwa rukuni-rukuni.
Rukuni na farko kai-tsaye sun tunkari Sansanjn Sojoji dake wata karamar makarantar sakandire dake da kimanin tazarar kilomita 500 daga garin, yayin da tawaga ta biyu kuma ta tare dukkan wasu muhimman hanyoyi da zasu kai ga shiga yankin.
Rukuni na uku kuma kamar yadda majiyarmu ta shaida mana sun shiga garin don dakatar dukkan wasu jami’an tsaro ko ’yan kato-da-gora ko matasa da zasu iya kokarin kawo musu cikas yayin harin.
Majiyar tace an kwashe kimanin sa’o’i biyu ana dauki-ba-dadi tun misalin karfe 4:00 na Asuba.