Maniyyata akalla 150 ne daga Karamar Hukumar Bida ta Jihar Neja ba za su sami sauke farali ba a bana bayan an zargi Jami’in Hukumar Alhazai (APO) na yankin, Nma Ndagana, da arcewa da kudaden kujerun da suka tura asusun ajiyarsa na banki.
Aminiya ta gano cewa maniyyatan dai sun tura miliyoyin kudaden kujerun nasu ne a asusun ajiyar jam’in na kashin kansa, maimakon a wanda hukumar alhazan ta tanada a bankin Jaiz.
- Abin da ya sa ba zan yarda na yi wa kowa Mataimaki ba – Kwankwaso
- Jamus za ta dawo wa Najeriya kayan tarihin da ta sace shekara 120 da suka wuce
Da wakilinmu ya tuntubi Sakataren Hukumar Jin-dadin Alhazai ta Jihar Neja, Alhaji Umar Maku Lapai, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka kafa kwamitin binciken lamarin.
Sai dai ya ce ba zai iya tantance hakikanin adadin mutanen da lamarin ya shafa ba, inda ya ce sun karbi korafe-korafe daban-daban, kuma har yanzu suna ci gaba da karba daga yankin.
Ya ce yawan mutanen da ya karbi kudaden nasu ya haura adadin kujerun da aka ware wa Karamar Hukumarsa, inda ya tura kudaden iya adadin wadanda ake bukata, ya sha kwana da na ragowar.
Sakataren hukumar ya ce, “Dangane da batun Karamar Hukumar Bida, Jami’in Alhazai na Yankin (APO) ya karbi kudin mutane sama da na wadanda aka ba shi. Wadanda suka biya kudinsu a hannunmu tuni mun ba su biza. Wadanda suka biya ta asusun ajiyarsa su ne masu matsala.
“Tuni muka kafa kwamitin da zai binciko mana hakikanin abin da ya faru, kuma har yanzu yana can yana bincike.
“Har yanzu masu korafin na zuwa rukuni-rukuni. A tashin farko, mun karbi korafin mutum 28, kuma har yanzu wasu na ci gaba da zuwa,” inji shi.
Alhaji Umar Lapai ya ce muddin suka gano akwai kamshin gaskiya a zarge-zargen da ake yi wa jami’in, to tabbas ba za su bar shi ya tafi Saudiyya ba, inda ya ce hukumar ba za ta dauki asarar duk kudaden da aka biya ta asusun da ba nata ba.
Sai dai ya kuma ce jigilar maniyyatan Jihar da a baya aka tsara za a rika yi daga filin jirgin saman Minna, babban birnin Jihar, yanzu an mayar da ita Babban Birnin Tarayya Abuja saboda dalilai na tsaro .