✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jamie Vardy ya tsawaita kwantaragin zama a Leicester City

Vardy zai shafe shekaru 14 yana taka leda a King Power idan ya cinye kwantaraginsa a Leicester City.

Dan wasan gaban Ingila, Jamie Vardy ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Leicester City zuwa karshen kakar 2024.

A watan Mayun da ya gabata ne Vardy mai shekara 35, ya cika shekara 10 a kungiyar King Power, inda ya ci kwallo 133 a Firimiyar Ingila cikin wasa 272 da ya haska.

Ya zura kwallo 24 a kakar wasanni ta 2015-16, inda kungiyar ta daga Firimiyar sannan ta kuma lashe kofin kalubale na FA.

A kakar ce Vardy wanda ya koma Leicester City daga Fleetwood a 2012, ya buga gasar Zakarun Turai, bayan cin Firimiyar Ingilar ta ba–zata.

Kafin wannan sabon kwantaragi, yarjejeniyar Vardy za ta kare a King Power a karshen kakar 2023, wanda aka yi ta alakanta shi da zai komawa Manchester United.

Vardy ya lashe takalmin zinari na yawan cin kwallaye a gasar Firimiyar Ingila a kakar 2019/20, lokacin da ya zira kwallaye 23 a raga.