✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar Maiduguri za ta kafa gidan tarihin tunawa da rikicin Boko Haram

Gidan tarihin zai taimaka wajen nuna wa jama'a illar yaki

Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas ta ce tana aiki da Jami’ar Maiduguri domin kafa gidan tarihin tunawa da rikicin Boko Haram a yankin.

Shugaban hukumar, Mohammed Alkali ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, inda ya ce kafa gidan zai taimaka wajen bayar da tarihin rikicin ta yadda zai canza tunanin mutane kuma ya amfane su.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya ta 2023 a Maiduguri.

Alkali ya kuma ce gidan zai ba masu ruwa da tsaki damar su samar da bayanai masu kyau da za su sa mutane su fahimci illar yaƙi a kan yankin da ma kasa baki ɗaya.

Ya ce kofar hukumar a bude take domin kowanne irin kokarin da zai taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addanci da tayar da ƙayar baya a yankin.

Tun da farko sai da shugaban kungiyar Jakadun Kungiyar Bunkasa Zaman Lafiya da Dogaro da Kai, Ahmed Shehu, ya nuna wa Alkali wasu ayyukan kirkira da wasu matasa da ba sa zuwa makaranta suka yi.

A nan ne shugaban ya nuna gamsuwarsa da kirkire-kirkiren, inda ya ce za su yi nazari a kan su sannan su taimaka wa wadanda ke bukatar a by kasa su.

%d bloggers like this: