✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba daidai ba ne tsine wa shugabanni saboda tsadar rayuwa – Sheikh Dahiru Bauchi

Ya ce a maimakon haka, kamata ya yi a koma ga Allah

Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, ya yi kira ga malamai a Najeriya da su guji furta kalaman da za su iya rarraba kan Musulmai ko yin barazana ga tsaron kasa.

Ibrahim, wanda kuma shi ne baban ɗan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, yayin da yake jawabi ga ’yan jarida a Bauchi, kan shirye-shiryen bikin Mauludi na bana.

Ya kuma roki mutane, musamman malamai, da su kauce wa muzanta juna da sunan wa’azi.

Ya ce mutuntawa da fahimtar juna da kuma amfani da dadaddiyar al’adar zaman lafiya sun zama wajibi muddin ana son samun ci gaba.

Sheikh Ibrahim ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su daina tsinewa shugabanninsu saboda matsin rayuwar da suke ciki a yanzu.

“Matsi da walwala duk daga Allah suke. Abin da ya kamata ’yan Najeriya su yi a wannan lokacin shi ne su koma ga Allah sannan su kyautata zaton abubuwa za su canza,” in ji malamin.