✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Jihar Gombe ta rantsar da sabbin likitoci 56

Jami'ar ta buƙaci sabbin likitocin da su zama jakadu nagari.

Jami’ar Jihar Gombe (GSU), ta rantsar da sabbin likitoci guda 56 da suka kammala karatunsu a bana, wanda ya kawo jimillar likitocin da jami’ar ta horar zuwa 185 cikin shekara biyar da suka gabata.

Shugaban Kwalejin Kimiyyar Lafiya na jami’ar, Farfesa Muhammad M. Manga ne, ya bayyana hakan a yayin bikin rantsar da likitocin karo na biyar.

Farfesa Manga, ya jinjinawa sabbin likitocin tare da shawartarsu su zama jakadu nagari na jami’ar.

A nasa jawabin, shugaban taron, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, wanda Farfesa Mu’azu Shehu Usman ya wakilta, ya taya sabbin likitocin murna tare da kiransu su fifita yi wa jihar da Najeriya hidima, duk da damarmakin aiki a ƙasashen waje.

Shi ma Magatakardar Hukumar Likitoci da Haƙora ta Najeriya (MDCN), Dakta Fatima Kyari, ta yaba wa jami’ar bisa ingantaccen tsarin karatun likitanci da ta samar.

Ta kuma ja hankalin sabbin likitocin kan muhimmancin gudanar da aikin asibiti da kulawa da marasa lafiya cikin tausayi.

A ƙarshe, Farfesa Idris Muhammad, wanda aka raɗa wa taron sunansa, ya yaba wa nasarorin da jami’ar ta samu.

Ya buƙaci sabbin likitocin su zama abin koyi a aikinsu da kuma bin ƙa’idojin aikin likitanci a kowane mataki.

Wannan bikin ya sake jaddada himmar Jami’ar Jihar Gombe, wajen samar da ƙwararrun likitoci da za su taimaka wa al’umma.