✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar ABU ta soma bincike kan asarar kashi 70 na gonakin kubewa a Najeriya

Za a iya amfani da ’ya’yan kubewar a girke-girke.

Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ce ta fara bincike kan sabuwar cutar da ta kama gonakin kubewa a fadin kasar nan.

Shugaban Cibiyar, Farfesa Muhammad Faguji Ishaku ya bayyana haka a zantawar sa da manema labarai a ofishin a Zariya.

Ya ce kwararrun cibiyar suna gudanar da bincike a dakin gwaje-gwajen cibiyar domin gano ko wace irin cuta ce kuma wadanne irin kwari ne ke yada cutar.

An gano wannan cuta ce da take kama gonakin kubewa a sassan kasar nan inda hakan ya janyo asarar sama da kashi 70 na kubewar.

Farfesa Ishaku ya ce bayan da cibiyar ta sami rahoton bullar cutar ne ta tura masana kimiyya zuwa sassan Jihar Kaduna da wasu bangarorin domin gano halin da ake ciki.

A cewarsa, cutar wata annoba ce domin ta yadu zuwa ko’ina kasar nan, kuma binciken gaggawa da masana kimiyyar cibiyar suka gudanar ya tabbatar da cewa kwayoyin cuta ce ke haifar da ita.

“Binciken masana ya nuna cewa kwari ne ke yada ita wannan kwayar cuta,wanda kuma an gano babu maganin feshi dake maganin ta”, a cewarsa.

Babban Daraktan ya ce hanyar da ya kamata a bi kawai ita ce a yi amfani da maganin feshi domin magance kwarin da hakan zai dakile yaduwar cutar.

Amma duk da haka, Farfesa Ishaku ya ce mutane za su iya yin amfani da ’ya’yan kubewar a girke-girke.

A don haka, ya shawarci manoma da su rinka fesa wa gonakinsu magunguna kafin su yi shuka kuma su rinka samo iri a wuraren da ya dace.