✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kayyade wa maniyyatan Yobe kujeru 1,960 na Hajjin 2024

Mafi karancin kudin ajiya da za a karba shi ne naira miliyan uku da dubu dari biyar.

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta tanadar wa maniyyatan Jihar Yobe kujeru 1,960 na aikin Hajjin shekara mai zuwa ta 2024.

Shugaban Hukumar Alhazai na Jihar Yobe, Mai Aliyu Usman ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manyan Jami’an Hukumar da masu karbar kudin ajiya na Kananan Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki na hukumar a dakin taro na hukumar da ke Damaturu.

Shugaban Hukumar ya shawarci wadanda suka yi ajiya na aikin Hajjin na badi, da su tabbatar da cewa kudin da suka ajiye na aikin Hajjin ya kai Naira 3,500,000.

Ya ce wannan adadin shi ne mafi karancin kafin-alkalmai da za a iya ajiyewa kafin Hukumar NAHCON ta kayyade kudin aikin Hajjin na badi.

Mai Aliyu ya bayyana cewa, saboda abubuwan da suke faruwa a halin yanzu, ana hasashen farashin aikin Hajjin bana zai haura sama da hakan.

Don haka ya jaddada bukatar maniyyata su cika ajiyar adadin da aka ambata kana su kuma jira sanarwar karshe na kudin Hajjin 2024 da NAHCON za ta fitar nan ba da jimawa ba in Allah Ya so.

Ya ci gaba da cewa, ana sa ran za a fara shirye-shiryen tunkarar aikin Hajjin badi nan ba da jimawa duk da cewar ko ya zuwa yanzu mai niyyar tafiya aikin Hajjin shekarar 2024 ya kawo kudin ajiyarsa za a karba.