Mahukunta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sun dauki sababbin matakai don tabbatar da tsaro a jami’ar a yayin da dalibai suka dawo don ci gaba da karatu.
Babban Jami’in Tsaro na Jami’ar, Malam Ashiru T. Zango ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya.
- Dan shekara 52 ya shiga hannu kan laifin kwanciya da ’yarsa
- Magidancin da ya nemi yada hoton tsiraicin matarsa ya shiga hannu
- Rikicin aure ne matsalar da aka fi kawo wa Hisbah a Kano
Ya ce a halin da ake ciki dukkan matakan da suka kamata a dauka don malamai da dalibai su samu natsuwa a fannin koyo da koyarwa an tanade su.
Malam Ashiru Zango ya ce bangaren tsaro na jami’ar ya hada hannu da jami’an tsaro da masu ruwa-da-tsaki kan harkar tsaro don samar da ingantaccen tsaro a lokacin da karatu ke gudana.
Ya ce sun kuma zauna da shugabannin al’umomin da ke makwabtaka da jami’ar, inda ya tabbatar wa daukacin ma’aikatan jami’ar cewa za su yi duk mai yiwuwa don samar da tsaro a makarantar.
“Amma sai kowa ya sanya hannu da ido da kuma fallasa duk abin da suka ga ba su gane ba,” inji shi.
Idan za a iya tunawa an kama wadansu da ake zargi da hannu a sace ma’aikatan jami’ar, wadanda ciki har da ma’aikacin sashin tsaro na jami’ar, mai suna Abubakar Aliyu da aka fi sani da Maigiwa.
Sauran wadanda aka kama tare da Maigiwa sun hada da wadansu makwabtan jami’ar, Abubakar Yakubu da aka fi sani da Dogo, da ke acaba a cikin jami’ar da Isiyaku Kabiru da aka fi sani da Mugu da Aliyu Bello da aka fi sani da Siniya, dukkansu mazauna Unguwar Biye da ke bayan jami’ar.
Wadanda ake tuhumar sun ambaci wadansu masu suna Sanusi da Maikudi da Shu’aibu a matsayin masu taimaka musu wajen satar mutane.