Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku.
Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana.
- An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe
- An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa
Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin.
Wata majiya da ke cikin tawagar ta tabbatar wa da wakilinmu faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Gwamnan ya je garin Wulgo ne tare da tawagarsa domin duba halin da tsaro ke ciki.
“A kan hanyarmu ta zuwa Maiduguri, bayan mun tashi daga Wulgo, lamarin ya faru,” in ji wata majiya.
Sautin harbe-harbe da aka yi ba zato ba tsammani ya haifar da firgici a cikin ayarin motocin, inda wasu ke ganin cewa harin kwanton ɓauna ne wadda ya sa ayarin motocin sun yi karo da ’yan ta’addar.
Wata majiya ta ce, ‘yan ta’addar sun harba makamin roka wanda bai fashe ba a lokacin da gwamnan ke jawabi.
‘Ɗaya daga cikin jami’an tsaro ya hango wani makamin roka da ’yan ta’addan suka harba a lokacin da gwamnan ke magana ga jama’a wanda ya sanar da tawagar da su bar wurin, akan hanyarsu ta fita ‘yan ta’addan sun yi artabu da jami’an tsaro,” in ji majiyar.
Jami’an tsaron da ke cikin ayarin motocin sun buɗe musu wuta tare da tarwatsa su bayan sun yi musayar wuta.
Wata majiya kuma ta ce ‘Alhamdu lillah, yanzu mun dawo Maiduguri.’
A cikin wannan batakashi majiyar da ke ayarin na cewa wasu daga cikin rundunar haɗin gwiwa ta farar hula da wasu mafarauta waɗanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun samu raunuka.