✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaron gidan yari sun harbe mutum biyu a Sakkwato

Jami’an tsaron gidan yari sun harbe wasu matasa guda biyu, Ibrahim dan Amarya Garge dan shekara 28 da Usman Umar Jallau Makerar Asada dan shekara…

Jami’an tsaron gidan yari sun harbe wasu matasa guda biyu, Ibrahim dan Amarya Garge dan shekara 28 da Usman Umar Jallau Makerar Asada dan shekara 33, a kan Titin Sarkin Musulmi Bello da ke Unguwar ’Yar Katanga cikin birnin Sakkwato, ranar Laraba da ta gabata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar gidan yari a Jihar Sakkwato, ASP Faruk ya yi magana da Aminiya kan lamarin. “An tare motar jami’anmu ce ta aiki da ta dauko wadanda ake zargi da laifuka daban-daban, mutum 18 za ta kai su kotu daga gidan yari; jami’anmu suna tare da ’yan sanda a lokacin.

“Bata garin suna dauke da muggan makamai suka yi kokarin kwatar wadanda muke tsare da su da aka kai kotu, a kan hanyar Sarkin Musulmi Abubakar, abin da ya sanya jami’an ’yan sanda suka taimaki jami’anmu don tabbatar da kudirin nasu bai samu nasara ba,” inji shi.

Haka kuma ya ce ’yan gidan yarin da aka dauko a motar, an samu nasara mayar da su cikin gidan yari ba da wata gardama ba.

“Konturola na Jihar Sakkwato, Haliru Nababa ya nuna gamsuwarsa da hadin kan jami’an tsaro da fatan hakan zai dore kuma ya tabbatar wa jama’a ci gaba da zaman lafiya tare kare hakkin wadanda ake tsare da su daidai da tsarin dokokin gidan yari na kasa,” inji ASP Faruk.

Aminiya ta kara samun bayani daga wani shaida yadda al’amarin ya faru, ya nemi a sakaya sunansa, ya ce motar gidan yarin ta lalace sai suka tsaya a Unguwar ’Yar Katanga. A cikin wadanda suka dauko akwai Area Boys din nan Mai Barewa, sai ya rika yin zikiri, mutane na kallonsa, sai jami’an suka nemi jama’a su bar wurin, suka ki. Sai suka rika yin harbi, kuma harsashi ya fada kan wadannan mutanen da ke kokarin wucewa, daya a kan babur, daya a kafa yake tafiya.

Aminiya ta ziyarci gidajen wadanda aka kashen, daya a Unguwar Garge, daya a Makerar Asada, inda wakilinmu ya samu an yi masu Sallah kamar yadda addini ya tanada. Iyayensu sun ce za su dauki matakin da suke ganin ya dace bayan sun kammala karbar gaisuwa da bayanan yadda yaransu suka rasa ransu.

Wata mai kama da wannan kuma, wasu yara matasa 13 suka rasa rayukansu a karamar Hukumar Goronyo, sanadiyyar karo da jirgin ruwansu ya yi da wani kwale-kwale, inda nan take ya birkice ya nutsar da su gaba daya kuma suka mutu. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya jajanta wa mahaifan mamatan a garin ’Yar Rimawa da ke cikin karamar Hukumar Goronyo.