✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato

An kashe su bayan sun kai ɗauki a wani ƙauye da ’yan ta’adda suka kai wa hari a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni

Mutum shida daga cikin Jami’an Tsaron Al’umma na Jihar Sakkwato sun kwanta dama bayan wata musayar wuta da ’yan bindiga a Kamarar Hukumar Sabon Birni.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari. A hanyarsu ne ’yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna.

Wata majiya ta bayyana cewa abokin aikinsu ne ya kira ya sanar da cewa, ’yan bindiga suna hanyarsu ta kawo hari ƙauyensi da ke kusa da Unguwan Lalle.

“Jami’an tsaron sun nemi abin hawa daga hukumar karamar hukumar amma an hana su, saboda an hana su gudanar da ayyukan tsaro na yau da kullum su kaɗai ba tare da jami’an tsaron gwamnatin ba,” in ji majiyarmu.

Da ba su samu abin hawa ba, sai suka hau baburansu suka tafi ƙauyen, amma aka yi rashin sa’a, ’yan bindigar suka yi musu kwanton ɓauna.

“Sna musayar wuta da ’yan ta’adda kafin a kashe mutum shida daga cikinsu, waɗanda daga bisani aka kawo gawarwakinsu an yi musu jana’iza,” in ji majiyar.

Lokacin da aka tuntube shi, kwamandan Rundunar Tsaro ta Jihar Sakkwato, Kanar Na-Allah Idris, ya ƙi cewa komai kan harin.

Haka nan, shugaban majalisa, Alhaji Ayuba Hashimu da memba mai wakiltar Sabon Aminu Boza sun kasa amsa kiran wayar wakilinmu.

Memba, wakiltar Sabon Birni gabas, ya tabbatar da lamarin amma ya ƙi yin ƙarin bayani saboda yankin ba a ƙarƙashinsa yake ba.

An tuntuɓi kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rafa’i, inda ya ce ba shi da rahoto kan lamarin.

Mai ba da shawara na musamman ga gwamna Ahmed Aliyu Ahmed kan sha’anin tsaro, Ahmed Usman ya tabbatar da harin, kuma ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.