✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun yi kadan a Najeriya —Abdulsalami

Ya yi kira da a dauki karin jami’an tsaro domin kawo karshen ta’addanci a kasar.

Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun yi kadan a kasar, lamarin da ya sa aka gaza magance matsalar tsaro da ake fuskanta a yanzu.

Janar Abdulsalami ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin ganawa da manema labarai a gidansa da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.

Ya yi kira da a dauki karin jami’an tsaro domin kawo karshen ta’addancin da ya dabaibaye kasar.

A cewarsa, daukar karin jami’an tsaron yana da muhimmanci la’akari da yadda wadanda ake da su a yanzu suke matukar shan wahala da hakan zai kawo nakasu wajen inganta ayyukansu.

Ya kuma jaddada bukatar samar da ingantattun kayan aiki ga jami’an tsaro domin su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata da kuma tabbatar da isasshen tsaro da aminci.

Tsohon Shugaban Kasar ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da ba da gudunmuwa ta hanyar mika duk wani rahoto da zai taimaka a inganta al’amuran tsaro a kasar.