✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun tarwatsa zanga-zangar da ta ɓarke a Kano

Kawo yanzu dai ba a gano dalilin zanga-zangar da ta ɓarke a ƙarƙashin Gadar Ƙofar Nasarawa ba.

Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da DSS sun tarwatsa zanga-zangar da ta ɓarke a Ƙofar Nasarawa da ke Jihar Kano.

Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun yi dandazo a ƙarƙashin gadar Ƙofar Nasarawa, lamarin da jami’an tsaron suka yi musu tarnaƙi da barkonon tsohuwa.

Kawo yanzu dai ba a gano dalilin gudanar da zanga-zangar ba, sai dai tuni jami’an tsaro suka sanya shamaki a hanyoyin da ke daura da zuwa Gidan Gwamnatin Kano.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ƙura ta lafa kuma kawo yanzu sun cafke mutum 17 da ake zargi na da hannu a lamarin.