Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da na ’yan sanda sun tarwatsa matasan da ke zanga-zanga kan matsalar kashe-kashen da ta addabi jama’a a Jihar Katsina.
Matasan dai sun taru ne a shatale-talen Kofar Soro da ke birnin Katsina, dauke da kwalaye masu rubuce-rubucen neman gwamnati a kawo karshen matsalar.
- ’Yan gudun hijirar Afghanistan 6 sun mutu a hatsarin mota a Iran
- Har tukin tasi na taba yi don tsira da mutuncina – Shugaban Kasar Rasha
Kafin zuwan jami’an tsaron dai, daya daga cikin jagororin zanga-zangar, Sakataren kungiyar Muryar Talaka, Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa, ya shaida wa ’yan jarida cewa suna zanga-zangar ne don jawo hankalin hukumomi su dauki matakin da ya dace wajen kawo karshen matsalar a Arewa da ma Najeriya baki daya.
“Yau babu wanda yake zaune cikin aminci. Kowa na sane da yadda aka yi wa Kwamshina Rabe Nasir kisan gilla, wanda hakan ke nuni da cewa hatta wadanda ke zaune a birane ba su tsira ba.
“Akwai mutane da dama da suke tsare a hannun masu garkuwa da mutane, mutum ba zai iya tafiya daga Katsina zuwa Sakkwato ta hanyar Jibiya ba saboda kalubalen tsaro,” inji shi.
Ita ma daya daga cikin masu zanga-zangar, Jamila Abbas ta ce mata ne suka fi shiga halin kaka-ni-ka-yi saboda matsalar tsaron.
To sai dai daga bisani jami’an tsaron sun tarwatsa masu zanga-zangar.
Yunkurin wakilinmu kan jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar, SP Gambo Isa don jin makasudin tarwatsa masu zanga-zangar ya ci tura.
Ko a makon da ya gabata, sai da daya daga cikin masu zanga-zangar a Kano ta janye bayan gayyatar da jami’an tsaron DSS suka yi mata.