Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da kuma ’yan sanda sun rufe sakatariyar jam’iyyar adawa ta PDP ta Jihar Ondo.
Hukumomin tsaron sun dauki matakin ne a safiyar Litinin a daidai lokacin da al’ummar jihar suke gunaguni da neman gwamnatin jihar ta bayyana musu inda Gwamna Rotimi Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki.
- Yadda Ba Da Dala Ga Masu Shigo Da Shinkafa Zai Shafi Farashin Ta Gida
- Ganduje ya lashi takobin kare kujerar gwamnan Nasarawa da kotu ta kwace
Ana zargin hukumomin tsaron sun rufe ofisihin jam’iyyar ne sakamakon shirin wasu ’yan jam’iyyar na gudanar da zanga-zanga kan rashin kasancewar gwamnan a jihar na tsawon lokaci.
Da farko Gwamna Akerodule wande ke fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba, ya shafe wata uku a kasar Jamus, inda yake jinya, kafin ya dawo jihar a watan Satumba.
Tun bayan dawowar gwamnan, ya ci gaba da zama a gidansa, da ke birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, lamarin da ya sa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar kiraye-kirayen ya sauka daga mukaminsa.
A ranar Lahadi PDP ta yi barazanar jagorantar wani gagarumin zanga-zanga a birnin Akure a yau Litinin, domin neman sanin inda Mista Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki da ya hana shi zama a Jihar Ondo.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani kan halin da ake ciki daga kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo Funmilayo Odunlami-Omisanya, amma hakar ba ta cim-ma ruwa ba.