Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Litinin.
Akwai dai rahotannin da ke cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kori Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni daga shugabancin riko na jam’iyyar.
- Mutum 5 sun mutu a wajen hakan yashi a Kano
- Gyaran Tsarin Mulki: Yadda Aisha Buhari ta ‘kasa’ fitar wa mata kitse a wuta
Rahotanni dai ne cewa akwai yiwuwar Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ne zai karbi ragamar daga hannun Buni.
To sai dai da yake tsokaci a kan lamarin, Sakataren riko na jam’iyyar, Sanata John James Akpanudoedehe ya ce har yanzu sune ke rike da ragamar jam’iyyar.
Ya ce, “An ankarar da mu kan wani labarin da wasu suka dauki nauyinsa kan cewa an samu sauyin shugabanci a Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC na Kasa.
“Wannan labarin sam babu kamshin gaskiya a cikinsa, ya kamata a yi watsi da shi. APC jam’iyya ce mai tsari, ba kara zube muke zaune ba. Ba a sanar da sauyin shugabanci ta bakin ‘wasu mutane’ da ba a bayyana sunansu a kafafen yada labarai.
“Muna kira ga magoya bayanmu da mambobin jam’iyyarmu da su ci gaba da goyon bayan jagorancin Mai Mala Buni don ganin an gudanar da babban taron jam’iyyarmu cikin nasara,” inji John James a cikin sanarwar.
A wani labarin kuma, jami’an tsaro sun toshe dukkan hanyoyin da ke zuwa unguwar Wuse 2 a Abuja, tare da tilasta wa masu ababen hawa canza hanya.
Wakilinmu ya lura cewa hatta ’yan jam’iyya da ma’aikatan sakatariyar ba a barin su su shiga ko su fita daga cikinta.
Wani dan sanda ya shaida wa wakilin namu cewa, “Mun zo nan ne don mu tabbatar da bin doka da oda.”