Jami’an tsaron hadin gwiwa sun karbe ikon majalisar dokokin jihar Jigawa a daidai lokacin da ake kokarin tsige kakakin majalisar Hon Aliyu Haruna Dangyating.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan majalisar na shirin tsige shugaban nasu ne saboda rashin gamsuwarsu da kuma zargin sa da yin babakere da yin gaban kansa wajen gudanar da harkokin majalisar da kuma rashin iya shugabanci.
Bincike ya nuna goyon bayan da akasarin mambobin majalisar suka samu kan tsige shi ya haifar da fargaba a garin Dutse, babban birnin jihar.
Jami’an tsaron da aka tura harabar majalisar sun hana kowa shiga har da ma’aikatan majalisar.
- Ya kamata Hukumar Kwastam ta sakar wa ’yan kasuwa mara — Sarkin Kano
- Kotu ta kwace N1.5bn daga tsohon shugaban NIRSAL
Wani babban jami’in majalissar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da an hana shi shiga harabar.
Matakin tsige shugaban Dangyating ya zo ne a daidai lokacin da yake kasar Saudiyya tare da gwamna Umar Namadi, a ziyarar da suka kai da nufin janyo masu zuba jari daga kasar zuwa jihar.
Da aka tambaye shi game da tsauraran matakan tsaro, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu Adam, ya ce sun samu bayanan sirri da ke nuna akwai barazana ga zaman lafiyar al’umma, lamarin da ya sa daukar matakan tsaro.