✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun kwato mutane 3, sun kashe dan bindiga a Kaduna

Yankin ya yi kaurin suna wajen hare haren ’yan bindiga musamman a ’yan kwanakin nan.

Jami’an tsaro sun samu nasarar kwato wasu mutum uku ciki har da wani jami’i na Ma’aikatar Kula da Dabbobi da ke Shika a Karamar Hukumar Giwa a sakamakon wani artabu da suka yi da ’yan bindiga.

Ganau sun sanar da cewa ma’aikacin mai Suna Mista Katung, an sace shi ne tare yaronsa guda daya kafin daga bisani aka dauki karin wani mutum guda.

Sahihan bayanai kuma sun tabbatar da dan bindiga daya ya rasa a yayin artabu da Jami’an tsaro, yayin da ’yan bindigar suka kai hari Kauyen Hayin Gada a gundumar Shika da ke Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Majiyar Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun kai harin ne misalin karfe 11 na daren Juma’a wayewar garin Asabar.

Bayaanai sun nuna cewa daruruwan jama’ar gari tare da taimakon jami’an tsaro ne suka fatattaki ’yan bindigar, lamarin da ya kai ga sun samu nasarar hallaka daya daga cikinsu.

Yankin Karamar Hukumar Giwa dai ya yi kaurin suna wajen hare haren ’yan bindiga musamman a ’yan kwanakin nan.

Sai dai mafi rinjayen mazauna na dangata hakan da kwararowar ’yan taddada daga jihohin Zamfara da Katsina wadanda jami’an tsaro suka hana sakat a can.