Jami’an tsaro sun kashe mutum hudu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Sudan, a cewar hukumomin lafiyar kasar.
Rahotannin farko sun nuna cewa jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar a birane da dama, ciki har Khatroum, babban birnin kasar.
- Dalilin da na gudu tun kafin Taliban ta kwace mulki – Tsohon Shugaban Afghanistan
- Najeriya A Yau: Yadda ’yan bindiga ke samun bayanan sirri
Zanga-zanga na ci gaba da kamari a kasar, inda ta faro tun a watan Oktoban 2021, sakamakon juyin mulki da kuma hambarar da gwamnatin kasar da sojoji suka yi.
Masu zanga-zangar sun bijire wa dokar kullen da aka sa inda suka fito kan tituta, wasu kuma suka tafi zuwa fadar shugaban kasa don nuna kin jininsu ga karbe mulkin da sojoji suka yi.
An katse layukan sadarwa a yunkurin hana mutane gudanar da zanga-zangar sannan an dasa sabbin na’urorin tsaro a manyan tituna.
Duk da haka an gudanar da irin wannan zanga-zanga a wasu biranen Sudan uku.
Halin matsin rayuwa, tsadar kayan masarufi na daga cikin wasu dalilan da suka sa dakarun sojin kasar suka karbe mulki daga hannun fararen hula.
Wasu bangarori daga al’ummar kasar na farin ciki da karbe mulkin, wasu kuma na da sabanin wannan ra’ayi.